logo

HAUSA

Kwararren Najeriya ya yi gargadin illolin dake tattare da siyasantar da batun binciken asalin COVID-19

2021-08-20 10:39:02 CRI

Kwararren Najeriya ya yi gargadin illolin dake tattare da siyasantar da batun binciken asalin COVID-19_fororder_210820-ahmad-Onunaiju

Wani kwararren masani daga Najeriya ya yi gargadin cewa siyasantar da batun aikin binciken gano asalin cutar COVID-19 ba zai taimaka wajen dakile annobar ba, kana zai iya gurgunta hadin gwiwar kasa da kasa wajen tsara matakan hada faruwar barkewar wata annobar a nan gaba.

Charles Onunaiju, daraktan cibiyar nazarin al’amurran kasar Sin dake Abuja, ya wallafa wani sharhi a ranar Talata a jaridar Vanguard da ake wallafawa a kasar, inda ya bayyana cewa, duk da kasancewar masana kimiyya sun bayyana cewa mai yiwuwa ne cutar COVID-19 ta samo asali ne daga min indallahi ba daga dakin gwaje gwaje ba, amma gwamnatin kasar Amurka tana ci gaba da jirkita batun asalin cutar wanda binciken masana kimiyya ya tabbatar inda take kokarin mayar da shi tamkar wani batu na yakin cacar baka don shafawa kasar Sin kashin kaza.

Masanin ya bukaci a koma kan turbar binciken masana maimakon yin shaci fadi, kasancewar zarge-zarge ba shi da wani alfanu kuma ba zai taimakawa hadin gwiwar kasa da kasa wajen kandagarkin hana yaduwar wata annobar a nan gaba ba.

Onunaiju ya ce, yayin da ake yada zarge zarge game da batun asalin cutar da kuma zargin kasar Sin da rashin bayyana lamarin a fili, ta bayyana a fili cewa zarge zargen da Washington ke yi tamkar wani salo ne na boye gazawarta wajen dakile cutar da kuma magance ta. (Ahmad Fagam)