logo

HAUSA

Adadin wadanda ke mutuwa sanadin COVID-19 na karuwa yayin da ake fuskantar barkewar Ebola da karin wasu cutukan

2021-08-20 11:50:51 CRI

Adadin wadanda ke mutuwa sanadin COVID-19 na karuwa yayin da ake fuskantar barkewar Ebola da karin wasu cutukan_fororder_210820-ahmad-5-west Afirka

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce a shiyyar yammacin Afrika an samu adadin mutanen da suka mutu sanadiyyar cutar COVID-19 mafi yawa tun bayan barkewar annobar, yayin da wasu kasashen da dama ke fama da matsalolin barkewar annobar kwalara, da Ebola da annobar zazzabin Marburg, wadanda ke kara haifar da barazana ga fannin ayyukan kai daukin gaggawa na dakile cutuka a shiyyar.

A cewar hukumar ta WHO, yawan mutanen da COVID-19 ta kashe a yammacin Afrika cikin makonni hudu da suka gabata ya karu da sama da kashi 193 bisa 100 daga mutane 348 a makonni hudu na baya zuwa mutane 1,018 a karshen wannan mako zuwa ranar 15 ga watan Augasta, hakan alamu ne dake nuna cewa tsarin kiwon lafiyar shiyyar yana fama da adadi mai yawa na majinyata.

Tsarin kiwon lafiyar yammacin Afrika ya fi fuskantar hadari sama da na sauran shiyyoyin. Hukumar WHO ta gudanar da wani bincike inda ta gano cewa tsarin kiwon lafiyar shiyyar yammacin Afrika yana da koma baya da kashi 21 bisa 100 idan an kwatanta da na shiyyar kudancin Afrika. (Ahmad)