logo

HAUSA

Yan sandan Najeriya sun kubutar mutane 11 daga masu garkuwa a arewa maso yammacin kasar

2021-08-19 09:51:06 CRI

Jami’an ’yan sanda a Najeriya sun yi nasarar kubutar da mutane 11 wadanda ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a makon jiya a jahar Zamfara dake shiyyar arewa maso yammacin kasar, kakakin hukumar ’yan sandan ya bayyana hakan.

Mohammad Shehu, kakakin ’yan sandan jahar Zamfara, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, ’yan sandan sun ceto mutane 11 wadanda ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a yankin Bakura dake jahar.

Shehu ya ce, wasu ’yan bindiga dake kyautata zaton barayi ne sun yi garkuwa da mutanen 11 a ranar Alhamis din da ta gabata a kauyen Yarkofoji dake karamar hukumar Bakura.

Ya ce a halin yanzu mutanen suna samun kulawar likitoci inda ake duba lafiyarsu gabanin a sada su da iyalansu.

A cewar kakakin, ’yan sanda suna aiki tukuru wajen ceto sauran mutanen dake hannun masu garkuwa a jahar. (Ahmad)