logo

HAUSA

Masana kimiyya sun yi kira da a sauya dabaru domin kare halittu daban daban

2021-08-18 12:34:54 CRI

Masana kimiyya sun yi kira da a sauya dabaru domin kare halittu daban daban_fororder_W020150522311363622460

Wani nazari da masana kimiyya a nahiyar Afrika suka fitar, ya bayyana cewa, cimma burin farfado da muhallin halittu daban-daban da kasashen duniya suka amince da shi, ya dogara ne da sauya manufofi da wadatar kudi da damawa da al’umma cikin aikin.

A cewar nazarin mai taken, “dunkule burikan farfado da muhallin halittu daga matakin karkara zuwa na duniya”, akwai bukatar gaggauta yi wa dabaru da dokokin da suka shafi kiyaye muhallin halittu gyaran fuska da tabbatar da suna mayar da hankali kan jama’a, haka kuma ana damawa da jama’a wajen aiwatar da su. Nazarin ya yi kira da a dauki mataki kan harkokin zaman takewa da na tattalin arziki dake lalata muhallin halittu, yana mai bayyana cewa, ya kamata karfafa juriyar al’ummu ya yi daidai da kiyaye halittu.

Masana kimiyya da masu rajin kiyaye halittu da suka shiga cikin nazarin, sun ce sakamakon taro karo na 15 na bangarorin da suka amince da yarjejeniyar MDD kan kare hallittu da muhallansu da za a yi a Kunming na kasar Sin daga ranar 11 zuwa 24 ga watan Oktoba, shi ne zai tantance yadda za a yi zaman jituwa tsakanin dan adam da sauran halittu.

Mataimakin shugaban gidauniyar kula da namun daji ta Afrika, Fred Kwame Kumah, ya ce dole ne kokarin kiyaye muhallin halittu a nan gaba, ya yi la’akari da bukatun zaman takewa da tattallin arziki da al’adun al’ummomi. (Fa’iza Mustapha)