logo

HAUSA

An kashe fararen hula 37 yayin wani hari a Nijer

2021-08-18 09:25:38 CRI

Kimanin fararen hula 37 aka kashe kana an raunata wasu hudu a wani harin da ’yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka kaddamar da yammacin ranar Litinin a kauyen Darey Dey, dake sashen Banibangou a  yankin Tillabery na jamhuriyar Nijer, wata majiyar jami’an tsaro ta tabbatar da faruwar harin da safiyar ranar Talata.

Majiyar ta ce, wasu gungun ’yan bindiga ne kan babura dauke da manyan makamai suka kaddamar da harin kan fararen hula a yayin da suke aiki a gonakinsu.

A shekarun baya bayan nan yankin Tillabery yana fuskantar karuwar munanan hare-hare da ake kaddamarwa kan dakarun tsaron kasar da kuma fararen hula. Daga farkon shekarar 2021, kimanin fararen hula 300 aka kashe a yankin, kamar yadda alkaluman hukumomi suka bayyana. (Ahmad)