logo

HAUSA

Nijeriya na yunkurin bunkasa zuba jari ta hanyar bayar da jinginar filayen jiragen sama

2021-08-17 11:12:40 CRI

Nijeriya na yunkurin bunkasa zuba jari ta hanyar bayar da jinginar filayen jiragen sama_fororder_210817-faeza 4-Nigerian Airports

Hukumomi a Nijeriya, sun fitar da ka’idojin bayar da jinginar filayen jiragen saman kasa da kasa 4 dake kasar, domin karfafawa bangarori masu zaman kansu gwiwar shiga a dama da su wajen zuba jari a bangaren raya ababen more rayuwa, da zummar habaka bangaren sufurin jiragen sama.

Cikin wata sanarwar da aka fitar a Lagos, birni mafi girma na kasar, babban sakataren ma’aikatar kula da sufurin jiragen sama ta kasar, Hassan Musa, ya ce ana sa ran yankunan dake kewaye da filayen jiragen saman za su habaka zuwa cibiyoyin cinikayya masu nagarta da samun riba da kuma dogaro da kai, lamarin da zai samar da guraben ayyukan yi da raya masana’antun gida ta hanyar shirin hadin gwiwa tsakanin gwamnati da bangarori masu zaman kansu.

Filayen jiragen saman 4 da ake magana, sun hada da na Abuja da Lagos da Kano da Fatakwal, wadanda su ne manyan biranen kasar wadda take da mafi yawan al’umma a Afrika. (Fa’iza Mustapha)