logo

HAUSA

Bambancin da ake nunawa musulmai a Amurka

2021-07-19 11:17:40 CRI

Bambancin da ake nunawa musulmai a Amurka_fororder_amurka

Kasar Amurka tana daukar kanta a matsayin “kasa mai bin tafarkin demokuradiya”, inda ta bayyana cewa, tana aiwatar da manufar tabbatar da daidaito tsakanin kabilu, da kuma ‘yancin bin addinai, amma hakika ba haka lamarin yake ba.

A shekaru da dama da suka gabata, gwamnatin kasar Amurka ta yi maraba da bakin da suka zo kasar daga sassan duniya, ciki har da musulmai, sakamakon karancin ‘yan kwadago, amma ya zama wajibi makauratan ba za su kawo illa ga moriyar fararen fata a kasar, haka kuma dole ne ba za su gurgunta mudarunsu ba. Amma sannu a hankali adadin musulmai a Amurka ya karu, a don haka Amurkawa fararen fata suke jin tsoron barazanar da musulmai za su iya kawowa, wannan ya sa suka dauki matakan nuna wariya da danniya da kayyade da gurgunta musulman dake rayuwa a kasar. Duk da cewa, adadin musulmai ya kai wajen miliyan 5 a Amurka, wato kaso 2 bisa dari kawai na daukacin al’ummun kasar, amma Amurkawa fararen fata ba sa hakuri da kasancewarsu a kasar.

Musamman ma bayan aukuwar harin ta’addanci na ranar 11 ga watan Satumban shekarar 2001, Amurkawa fararen fata suna kara jin tsoron musulmai, har suna mayar da musulmai da addinin musulmi a matsayin masu hadari wanda zai kawo musu barazana, a sanadin haka, a kan gudanar da bincike kan musulmai, ko hana su shiga jiragen sama, ko kuma soke tallafin kudin da gwamnatin kasar take samar musu, wani lokaci kuwa, akan rufe asusun bankuna na musulmai ba gaira da dalili, har ma a kai su kara ba tare da gabatar da laifi ba, an lura cewa, musulmai dake rayuwa a Amurka, suna kara fama da kadaici sakamakon mayar da su saniyar ware.

Amurka ta kan bayyana cewa, tana gudanar da harkokinta bisa doka, saboda haka, ta saba da kayyade musulmai ta hanyar kafa doka, musamman ma bayan aukuwar harin ta’addancin ranar 11 ga watan Satumban shekarar 2001, an hanzatar da aikin kafa dokar yin adawa da musulmai a fadin kasar.

Kana gwamnatin Amurka ita ma ta kan fitar da manufar kayyade hakkin musulmai kai tsaye, alal misali umurni mai lamba 13769 da gwamnatin tarayyar kasar ta fitar, a ranar 27 ga watan Janairun shekarar 2017, a wannan rana, shugaban kasar Amurka na wancan lokaci Donald Trump ya sa hannu kan umurni mai taken “shirin kare tsaron kasa ta hanyar hana shigowar ‘yan ta’addan ketare”, inda aka bayyana cewa, a cikin kwanaki 90 masu zuwa, an hana mutane ‘yan asalin kasashe bakwai wadanda suka hada da Iraki da Syria da Iran da Sudan da Somaliya da Yemen da Libya su shiga Amurka, wannan na nuna cewa, umurnin ya kwace hakkin musulman kasar na haduwa da dangogi da musanyar addini da kuma cudanyar al’adu da sauransu, yanzu haka duk da cewa, gwamnatin Joe Biden ta dakatar da umurnin bisa la’akari da moriyar kanta, amma manufar tana ci gaba da yin tasiri ga yanayin rayuwar musulmai, kana ya tono ainihin yanayin demokuradiya da Amurka ke ciki.

Ban da haka, an nuna bambanci mai tsanani ga musulmai yayin da suke neman guraben aikin yi, alkaluman binciken da jami’ar Carnegie Mellon ta fitar a shekarar 2013 sun nuna cewa, amsar sakwannin da za a baiwa musulmai wadanda suka gabatar bukatar neman aikin yi ba su kai kaso 87 bisa dari ba, idan an kwatanta da sakon da Amurkawa masu bin addinin Kirista ke samu.

Hakazalika, karar da aka kai kotu dangane da matsalar addini tana karuwa, har an hana musulmai mata su daura kwali, an ce, an hana wasu musulmai mata shiga wurin taron jama’a idan suka daura nikabi. A watan Oktoban shekarar 2019, an wata ‘yar wasa musulma mai shekaru 16 daga jihar Ohio ta kasar shiga gasa, bisa dalilin daure nikabi.

Alkaluman da aka fitar sun nuna cewa, duk da cewa, adadin musulmai kaso 2 bisa dari ne kawai a Amurka, amma adadin al’amuran nuna wariyar addini kaso 25 bisa dari ne suka faru a kan musulmai.

Ana iya cewa, ana take hakkin halal na musulmai a Amurka, alkaluma sun nuna cewa, kafin shekarar 2001, matsakacin adadin laifuffukan nuna adawa da musulmai a kasar a kowace shekara ya kai 31, amma bayan shekarar, wato bayan aukuwar harin ta’addanci na ranar 11 ga watan Satumban shekarar, adadin ya karu zuwa 546.(Jamila)