logo

HAUSA

An damu game da gazawar gwamnatin Amurka kan hadarin rushewar gini

2021-07-04 16:46:43 CRI

An damu game da gazawar gwamnatin Amurka kan hadarin rushewar gini_fororder_amurka

Kafin faruwar wannan ibtila’in, al’ummun kasa da kasa sun nuna damuwa matuka da ganin yanayin da kasar Amurka ke ciki yayin kandagarkin annobar cutar numfashi ta COVID-19, yanzu kuma sun sake nuna damuwa game da gazawar gwamnatin kasar kan hadarin rushewar ginin da ya faru a jihar Florida kafin kwanaki goma da suka gabata, wato gwamnatin kasar ta Amurka ba ta dauki matakin ceton rayuka cikin lokaci ba.

Alkaluman da gwamnatin kasar Amurka ta samar sun nuna cewa, ya zuwa ranar 2 ga wata, adadin mutanen da suka rasu a cikin hadarin ya kai 22, kuma akwai sauran wasu mutanen 126 sun bace, wato ba a san inda suke ba.

Kafofin watsa labarai na kasar su ma sun bayyana cewa, bayan aukuwar hadarin, an shafe awoyi 16 domin neman amincewar samun kayayyakin ceto daga hukumomin gwamnatin da abin ya shafa, wato tawaga ta farko dake kumshe da masu aikin ceto goma da wani abu ne kawai ta isa wurin da hadarin ya auku bayan awoyi 16.

Daga Amurkawa sama da dubu 600 da suka rasa rayuka sakamakon barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19, zuwa mutanen da suka rasu a hadarin rushewar gini a jihar Florida, an lura cewa, wasu ‘yan siyasar Amurka ba su nuna tausayi ko kadan kan hakkin rayuka, wato hakkin bil Adama mafi muhimmanci, to yanzu ko suna da bakin maganzar sake zargin sauran kasashe bisa fakewa da hakkin bil Adama? (Jamila)