logo

HAUSA

Hukuncin Da Aka Yanke Wa Chauvin Bai Boye Mummunan Halin Da Amurka Ke Ciki Wajen Kare Hakkin Dan Adam Ba

2021-06-27 20:34:42 CRI

Hukuncin Da Aka Yanke Wa Chauvin Bai Boye Mummunan Halin Da Amurka Ke Ciki Wajen Kare Hakkin Dan Adam Ba_fororder_us

Kwanan baya, an sanar da hukuncin da aka yankewa Derek Chauvin, dan sandan kasar Amurka farar fata wanda ya kashe George Floyd wani Ba’amurke dan asalin Afirka. Iyalin Floyd da ma dukkan Amurkawa wadanda aka nuna musu wariyar launin fata sun sake jin bakin ciki.

A baya da kyar aka yanke wa ‘yan sandan Amurka hukunci a Amurka, wadanda suka kashe fararen hula yayin da suke aiwatar da doka ta hanyar amfani karfin tuwo. Wasu kafofin yada labaru na Amurka sun yi shelar cewa, hukuncin dauri a gidan kurkuku da aka yankewa Chauvin na tsawon shekaru 22 da rabi, wata muhimmiyar alama ce a tarihin ‘yan sandan Amurka ta fuskar aiwatar da doka. Amma Amurkawa masu dimbin yawa ba su yi tsamanin haka ba.

A ganin wasu mutanen Amurka, babu wanda ya amince da hukuncin. Ya zuwa yanzu Chauvin bai nemi gafara daga iyalin Floyd ba tukuna, haka kuma ba za a iya canza yadda ake nuna wariyar launin fata a Amurka ba sakamakon wani batu. A shekara guda da ta gabata, ba a hana ‘yan sandan Amurka su aiwatar da doka ta hanyar nuna karfin tuwo ba, ba a kuma dakatar da nuna wariyar launin fata a Amurka ba. Ya zuwa yanzu ana ta fama da matsalar nuna wariyar launin fata a sassa daban daban Amurka. Alkaluman wani shiri mai zaman kansa na Amurka wato “Taswirar bayyana yadda ‘yan sanda suka nuna karfin tuwo” sun nuna cewa, a shekarar 2020, mutane 1126 da ‘yan sanda suka kashe a Amurka, kaso 28 cikin 100 ‘yan asalin Afirka ne, adadin da ya fi rabin jimillar yawan mutanen Amurka na kaso 13 cikin 100 yawa.

Yanzu haka fararen fata suna fi nuna fifiko a fannoni daban daban a Amurka. Har ila yau wasu ‘yan siyasa ba su yi kome ba, har ma sun rura wuta a fili. Ana ta nuna wariyar launin fata daga dukkan fannoni kuma bisa tsari a Amurka. Amma abin takaicin shi ne wasu ‘yan siyasan Amurka sun kau da kai daga yadda ake keta hakkin dan Adam a kasarsu, sun sossoki sauran kasashe bisa hujjar hakkin dan Adam.

A yayin taron kwamitin hakkin dan Adam na MDD karo na 47, Amurka ta hada kai da tsirarrun kasashen yammacin duniya sun bata sunan kasar Sin bisa hujjar Xinjiang, Hong Kong da Tibet. Amma kasashe fiye da 90 sun bayyana goyon bayansu ga kasar Sin ta hanyoyi daban daban tare da amsa kiran kasar Sin, inda suka ki yarda da sanya siyasa kan batun hakkin dan Adam da yin amfani da ma’auni biyu kan batun. Kasar Ukraine ta riga ta soke sa hannu kan jawabin hadin gwiwa ta adawa da kasar Sin a yayin taron.

Hakikanin abubuwa sun shaida cewa, Amurka da wasu tsirarrun kasashen yammacin duniya sun sake gazawa a yunkurinsu na bata sunan kasar Sin. Sabanin hakan, an sossoki yadda ake keta hakkin dan Adam a wadannan kasashe a yayin taron. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan