logo

HAUSA

An yankewa tsohon jami’in dan sandan Amurka Derek Chauvin hukuncin zaman gidan kaso na shekaru 22.5 saboda kisan George Floyd

2021-06-26 17:49:29 CRI

An yankewa tsohon jami’in dan sandan Amurka Derek Chauvin hukuncin zaman gidan kaso na shekaru 22.5 saboda kisan George Floyd_fororder_d01373f082025aafa2716cedf64b1d6c024f1a86

A ranar Juma’ar da ta gabata aka yanke wa tsohon jami’in dan sandan kasar Amurka Derek Chauvin, hukuncin zaman gidan kaso na watanni 270, daidai da shekaru 22 da wata biyar, sakamakon kisan da ya yiwa bakar fatar nan dan Amurka George Floyd a shekarar bara a birnin Minneapolis, na jahar Minnesota.

Chauvin shi ne jami’in dan sanda farar fata na farko a jahar Minnesota da ya fuskanci hukuncin zaman gidan yari sakamakon kashe bakar fata, kamar yadda gidan rediyon al’umma na jahar Minnesota ya bayyana.

Iyalan marigayi Floyd sun halarci zaman kotun a lokacin sauraron karar.

A lokacin zama na farko na shara’ar, alkalin kotun yankin Hennepin, Peter Cahill, ya yanke hukuncin tuhumar Chauvin da laifin tozarta hakkin da hukuma ta dora masa, a matsayinsa na jami’in dan sanda, kuma ya nuna halayyar rashin Imani, a lokacin da ya makure wuyan Floyd da gwiwarsa har na sama da mintoci 9 bayan da ya tsare shi. Daga bisani an sanar da mutuwar Floyd a asibiti.

Mutuwar Floyd ta haifar da zazzafar zanga-zangar da aka shafe makonni ana gudanarwa a sassan duniya domin nuna kin amincewa da halayyar rashin imanin da dan sandan ya nunawa gami da nuna wariyar launin fata a shekarar bara.(Ahmad)