logo

HAUSA

Sin ta yi Allah wadai da mu’amalar soji tsakanin Amurka da Taiwan

2021-06-25 11:11:54 CRI

Sin ta yi Allah wadai da mu’amalar soji tsakanin Amurka da Taiwan_fororder_0625-AH3-AmurkaTaiwan

Kakakin hukumar sojojin kasar Sin ya ce, kasar ta yi Allah wadai da duk wata mu’amalar soji ko kuma tuntuba tsakanin Amurka da Taiwan.

Ren, ya bukaci Amurka ta kiyaye manufar nan ta kasar Sin daya tak da dokar dake karkashin yarjejeniyoyi uku na hadin gwiwar Sin da Amurka  kuma ta kaucewa duk wata mu’amalar soji tsakaninta da Taiwan.

A cewar Ren, ya kamata hukumar gudanarwar jam’iyyar Taiwan's Democratic Progressive Party (DPP) su sani cewa makomar yankin Taiwan ta dogara ne da hadin kan kasa kana kyautatuwar zaman rayuwar al’ummar Taiwan ya dogara ne kan sauye-sauyen bunkasa ci gaban kasa.

Atisayen sojoji da rundunar sojoji ta PLA ta gudanar a yankin Taiwan ya zama tilas bisa lura da yanayin da ake ciki a halin yanzu a yankin da kuma tabbatar da zaman lafiyar yankin da tabbatar da ikon mallakar yankunan kasa.

Ya ce rundunar sojoji ta PLA za ta cigaba da sauke nauyin dake bisa wuyanta na tabbatar da zaman lafiya da kiyaye ikon yankunan kasar kana da tabbatar da kiyaye tsaron kasa. (Ahmad)