logo

HAUSA

Menene ma’anar “sabo” a cikin sabon tsarin jam’iyyun siyasar kasar Sin?

2021-06-25 21:42:25 CRI

Menene ma’anar “sabo” a cikin sabon tsarin jam’iyyun siyasar kasar Sin?_fororder_AA

A yayin da ake dab da cikon shekaru 100 cif da kafa jam’iyyar kwaminis mai mulkin kasar Sin, gwamnatin kasar ta gabatar da takardar bayani mai taken sabon tsarin jam’iyyun siyasar kasar, abun da ya baiwa kasa da kasa damar kara fahimtar tsarin jam’iyyun siyasa da tsarin siyasar kasar.

Ke nan, menene ainihin ma’anar kalmar “sabo” a cikin sabon tsarin jam’iyyun siyasar kasar Sin?

Na farko, akwai alaka ta musamman tsakanin jam’iyyun siyasa daban-daban a kasar. Wato sabon tsarin jam’iyyun siyasar kasar Sin ya kunshi jam’iyyar kwaminis da jam’iyyun demokuradiyya guda 8, gami da al’umma da ba na kowace jam’iyya ba.

Jam’iyyar kwaminis, jam’iyya ce mai mulkin kasar Sin, amma su jam’iyyun demokuradiyya ba jam’iyyun ‘yan hamayya ba ne karkashin tsarin siyasar kasashen yammacin duniya, jam’iyyu ne dake halartar harkokin siyasar kasar karkashin shugabancin jam’iyyar kwaminis.

Na biyu, kalmar “sabo” cikin sabon tsarin jam’iyyun siyasar kasar Sin na nufin hanya ta musamman da ake bi, wajen tsara manufofi da daukar matakan mulki.

Akwai matakai gami da gungun mutane daban-daban a kasar Sin, inda jam’iyyar kwaminis da jam’iyyun demokuradiyya 8 gami da al’umma da ba na kowace jam’iyya ba, suke wakiltar mutane daga bangarori daban-daban, abun da ya tabbatar da cewa, sabon tsarin ya girmama muradun mutane masu rinjaye, da la’akari da bukatar mutane marasa rinjaye, wato ya iya wakiltar muradun mutane daga bangarori daban-daban.

A nasa bangaren, babban manazarci daga jami’ar Cambridge dake kasar Birtaniya, Martin Jacques ya bayyana cewa, kasashen yammacin duniya suna ganin cewa, tsarin kasancewar jam’iyyun siyasa daban-daban yana taimakawa ga raya tsarin demokuradiyya, amma hakikanin gaskiya ita ce, jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin tana da nata dabaru na samun karfi da kuzari, amma jam’iyyun siyasar kasashen yamma suna kara nisanta daga al’ummomin da suke wakilta.

Sabon tsarin jam’iyyun siyasa yana taka muhimmiyar rawa ga raya harkokin siyasa da na zaman rayuwar al’umma, al’amarin da ya shaida cewa, babu wani tsarin jam’iyyun siyasa a duniya, wanda ya dace da kowace kasa, sai dai tsarin jam’iyyun siyasar da ya dace da hakikanin halin da ake ciki a wata kasa, shi ne tsari mai nagarta. (Murtala Zhang)