logo

HAUSA

Dalilin da ya sa ake samun labaran karya

2021-06-07 15:26:32 CMG

Dalilin da ya sa ake samun labaran karya_fororder_d009b3de9c82d1581f6c3c53a35b7bdebd3e4239

Kwanan baya, wasu ‘yan majalisun dokokin kasar Amurka 209 sun rubuta wasika ga shugabar majalisar wakilai ta kasar Nancy Pelosi, tare da neman bukatar a zartas da wani kuduri na kalubalantar kasar Sin, don ta dauki alhakin “haddasa yaduwar cutar COVID-19 a duniya” tare da biyan diyya. Ko da yake, binciken da hukumar lafiya ta duniya WHO ta yi bai nuna cewa cutar Covid-19 ta samu asalinta a kasar Sin ko kuma kasar tana da wani laifi game da yaduwar cutar ba, duk da haka wadannan ‘yan majalisar dokokin kasar Amurka sun tsaya kan dora laifin “haddasa yaduwar annoba” kan kasar Sin.

Da wuya ne a ce su wadannan ‘yan majalisun kasar Amurka sun gaskata wannan zargi, ko kuma sun yi hakan saboda kin jinin kasar Sin kawai, da neman hana kasar Sin samun ci gaba. Hakika mahukuntan kasar Amurka sun riga sun maida “takara” da “taho mu gama” a matsayin babban jigon huldar dake tsakanin kasar Sin da kasar Amurka. Yanzu ana tantance wani shirin dokar takara da kasar Sin a majalisun dokokin kasar Amurka, inda ake neman takurawa kasar Sin a fannonin diplomasiyya, da aikin soja, da kimiyya da fasaha, da dai sauransu. Har ma kasar na neman ware dalar Amurka miliyan 300 musamman ma domin bata sunan kasar Sin, da shafa mata kashin kaza.

A fannin diplomasiya, Antony Blinken, sakataren harkokin wajen kasar Amurka, ya gabatar da manufar neman hada baki da tsoffin kawayen kasar Amurka, a kokarin takurawa kasar Sin. Sai dai Amurka ta taba kebantar da wadannan kasashe, bisa manufar da tsohon shugaban kasar Donald Trump ya gabatar, ta “maida moriyar kasar Amurka gaban ta sauran kasashe”. Yanzu mene ne matakin da Mista Blinken zai dauka don sake janyo hankalin tsoffin kawayen kasarsa?

Alkaluma sun nuna cewa, wasu kasashe 165 na kallon kasar Sin a matsayin abokiyar hulda mafi muhimmanci a fannin ciniki, yayin da wasu kasashe 13 kawai suke kallon kasar Amurka a matsayin babbar abokiyar hulda ta cinikayya. Sa’an nan wasu kasashe fiye da 100 na hadin gwiwa da kasar Sin wajen gudanar da manyan ayyuka fiye da 2600 karkashin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, wadanda darajarsu ta kai dala trilian 3.7. Yayin da a nata bangaren, abun da kasar Amurka take yi ya kebanci kokarinta da nuna damuwa a duniya kawai, wai akwai hadarin “tarkon cin bashi”.

A zahiri ne, kasar Amurka ba ta da isashen karfi wajen takara da kasar Sin, musamman ma a fannin taimakawa sauran kasashe samun ci gaba, ta hanyar hadin gwiwa a bangaren ciniki, ko kuma gina manyan kayayyakin more rayuwa. Don haka kasar na fuskantar wahalhalu, yayin da take kokarin lallashin kasashe daban daban domin su kulla kawance da kasar Amurkar, ganin yadda ta kasa nuna musu hakikanin moriyar da za su samu. Saboda haka, kasar Amurka ta dauki wani mataki maras mutunci: wajen yada jita-jita game da kasar Sin, don sanya sauran kasashe su kyamace ta.

Muna cikin wani lokaci ne na yawan samun labaran kanzon kurege, inda aikin bata sunan wata kasa ba shi da wuya, illa tsamo wasu maganganu ba tare da tantance su ba, da kambama wasu batutuwa, gami da yada jita-jita da karairayi kai tsaye. Misali, BBC Hausa ta taba watsa wani labari a kwanan baya, inda ta ce hukumar kasar Sin na yin amfani da fasahohin zamani masu alaka da kyamara ta CCTV wajen sa ido kan tunanin mutane ‘yan kabilar Uygur dake jihar Xinjiang ta kasar, da yanke musu hukunci bisa duk wani bayanin da aka samu ta kyamarar. Amma a hakika fasahohin dan Adam ba su kai wani matsayi na iya bambanta tunanin mutane ta hanyar binciken hotunansu ba, kana idan kasar Sin ta yanke hukunci kan mutanen kasar yadda ta ga dama, to, ba zai yiwu ta samu damar raya tattalin arzikinta cikin matukar sauri ba. Ta haka za mu iya ganin cewa, BBC ta kirkiro wata karya ce kawai, wadda ba ta kunshi hakikanin bayani ba: kawai ta tsamo maganar wani “injiniyan kwamfuta”, wanda ta ce ta kasa bayyana sunansa da wurin aikinsa. Duk da haka wannan labari na karya ya yaudare mutane da yawa, wadanda suka fara watsa wannan labari a shafukan yanar gizo ta Internet, tare da nuna fushi ga kasar Sin.

A wannan karo, kasar Amurka a nata bangare tana neman kirkirar wani babban labarin jabu, da zai zama tamkar wani wasan kwaikwayo, inda shugaba Joe Biden na kasar ya umurci hukumar leken asiri ta kasar da ta fara binciken asalin cutar COVID-19, da gabatar da wani rahoto cikin kwanaki 90. Dalilin da ya sa ya ba hukumar leken asiri wannan aiki, maimakon hukumomi na kimiyya da na aikin lafiya shi ne, domin hukumar leken asiri ta kasar ta fi kwarewa a fannin samar da bayanai na jabu. Da ma hukumar ta taba gabatar da shaidar mallakar makaman kare dangi a hannun Saddam Hussein na kasar Iraki, don baiwa kasar Amurka dalilin kaddamar da yaki a kasar Iraki. Sai dai a karshe dai, an gano cewa hukumar ta ba da shaida ce ta jabu kawai, bayan sojojin kasar Amurka sun riga sun kashe dubun-dubatar jama’ar kasar Iraki. Batun nan ya amsa  maganar da tsohon shugaban hukumar leken asiri ta CIA ta kasar Amurka, Mike Pompeo, ya fada, wato “CIA tana yin karya, tana cutar mutane, da satan bayanai. Har ma tana tsara darussa don horar da ma’aikatanta da wadannan fasahohi. Hakan wani abun alfahari ne na kasar Amurka.”

Abun da za a iya hasashe shi ne, hukumar leken asiri ta kasar Amurka za ta tsara wani rahoto, wanda zai kunshi cikakkun bayanai game da “laifukan da kasar Sin ta aikata”. Zuwa wancan lokaci, kasar Amurka da wasu kasashen yammacin duniya za su kara kokarin diran mikiya wa kasar Sin. Abun da ya kamata mu yi shi ne mu maida hankali kan sakamakon binciken da hukumar lafiya ta WHO da sauran manyan kungiyoyi masu nazarin kimiyya da fasaha suka gabatar, don magance baiwa wasu mutane damar cusa wasu karairayi da bayanai na jabu a cikin kwakwalwarmu. (Bello Wang)

Bello