logo

HAUSA

Mista Antony Blinken, dan Allah ka amshi kiran da masu amfani da Intanet suka yi na sakin Julian Paul Assange

2021-06-05 17:37:34 CRI

Mista Antony Blinken, dan Allah ka amshi kiran da masu amfani da Intanet suka yi na sakin Julian Paul Assange_fororder_微信图片_20210605163220

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya wallafa wani bayani a shafinsa na Twitta, inda ya bukaci ‘yan sandan yankin Hong Kong su saki wasu mutanen da suka kama, sakamakon halartar wani gangamin da ya sabawa doka. Akwai wasu masu amfani da kafar sada zumunta ta Twitta wadanda suka amsa masa da cewa, ya kamata Amurka ta saki mutanen da ta kama ko gurfanar da su gaban kuliya, sakamakon abun da suka yi na bankado makarkashiyar gwamnatin kasar, har ma sun yi kira da a soke bukatar neman mayarwa kasar Julian Paul Assange, wanda ya kafa tashar Intanet ta WikiLeaks.

Antony Blinken ya nuna yatsa game da matakan da ‘yan sandan Hong Kong suka dauka bisa doka, tare da yunkurin wanke wasu mutane daga laifuffukan da suka aikata, amma ya yi biris da bukatar da aka yi masa na sakin Julian Assange, duk da cewa asirin da ya tona gaskiya ne. Ya kamata Amurka ta ji kunya saboda nuna fuska biyu da ta yi a bangaren doka, duba da abun da take alfahari da cewa, wai ita kasa ce mai mutunta doka da oda.

Mista Antony Blinken, dan Allah ka amshi kiran da masu amfani da Intanet suka yi na sakin Julian Paul Assange_fororder_70477170

A kofar kotun da aka saurari karar Assange dake kasar Birtaniya a watan Janairun bana, mutane sun yi ihu “’Yanci! ‘Yanci!”, inda suka nemi a sake shi ba tare da bata lokaci ba. Tambayar a nan ita ce, shin da gaske ‘yan siyasar Amurka kamar shi Antony Blinken ba su ji bukatarsu ba? Har kullum suna fakewa da batun “demokuradiyya” da “’yanci” don marawa masu tada zaune-tsaye a Hong Kong baya, amma me ya sa suka yi watsi da bukatar al’ummarsu na neman ‘yanci da demokuradiyya? Sabili da haka, Mista Antony Blinken, ya dace ka dakatar da maida hankali kan batun yankin Hong Kong, wanda ya yi maka nisan gaske, ka karkata hankalinka zuwa ga yadda za ka yi don amsa bukatar masu amfani da Intanet ta sakin Julian Assange! (Murtala Zhang)