logo

HAUSA

Mista Antony Blinken, dan Allah ka tsaya tare da al’ummar Amurka!

2021-06-04 21:18:14 CRI

Mista Antony Blinken, dan Allah ka tsaya tare da al’ummar Amurka!_fororder_A

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya fitar da wata sanarwa a yau Jumma’a, inda ya nuna yatsa ga batun hakkin dan Adam na yankin Hong Kong na kasar Sin, tare da bayyana cewa wai zai kasance tare da al’ummar kasar Sin. Kash! Wannan abin dariya ne .

A gaskiya, Antony Blinken ya yi biris da ainihin halin da kasarsa take ciki, wato yawan mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon cutar COVID-19 ya zarce dubu 600 a Amurka. Haka kuma ya yi biris da hakikanin halin da ake ciki a yankin Hong Kong, wato ganin yadda aka fara aiwatar da wasu muhimman dokoki tun bayan da Hong Kong ta dawo babban yankin kasar Sin a shekara ta 1997, ciki har da babbar doka ta Hong Kong, da babbar dokar tsaron kasa ta yankin, tare kuma da daukar jerin kyawawan matakai ciki har da inganta tsarin zabe na Hong Kong, an kara samar da tabbaci ga hakkoki gami da ‘yanci na mazauna Hong Kong. Maimakon haka, Antony Blinken ya sha fake da batutuwan da suka shafi “demokuradiyya” da “hakkin dan Adam”, don yin shisshigi a harkokin yankin Hong Kong, har ma da harkokin cikin gidan kasar Sin. Wannan ya shaida cewa, wasu ‘yan siyasar Amurka sun maida muradunsu na siyasa a gaban kome, ciki har da lafiyar al’umma.

Mista Antony Blinken, dan Allah ka tsaya tare da al’ummar Amurka!_fororder_B

Irin wannan wayo na Antony Blinken da na sauran wasu ‘yan siyasar Amurka, ya jaddada cewa, Amurka na son yin babakere maimakon abun da take furtawa wato kare hakkin dan Adam. Babatun da Amurka take yi game da tsarin demokuradiyya da kare hakkin dan Adam, shi ke kara nunawa duniya halayyar muguntarta!

Kamata ya yi Mista Antony Blinken ya tsaya tare da al’ummar kasarsa, ya kula da lafiya da rayuwarsu!(Murtala Zhang)