logo

HAUSA

Kariyar Japan ba za ta iya yaudarar al’ummun kasa da kasa ba

2021-05-29 16:13:02 CRI

Kariyar Japan ba za ta iya yaudarar al’ummun kasa da kasa ba_fororder_japan

Ofishin jakdancin kasar Japan, ya ba da amsa kan wasu tambayoyin da suka shafi batun zubar da dagwalon cibiyar sarrafa sinadarin nukiliya dake Fukushima a shafinsa na yanar gizo, inda ya bayyana cewa, ruwan da kasarsa za ta zubar cikin teku ba ruwan dagwalon nukiliya ba ne, ruwa ne na nukiliyar da aka sarrafa wato ALPS, yana mai cewa, bisa ka’idar kasa da kasa, kasashen duniya daban-daban na zubar da irin ruwan a cikin teku.

Yanzu haka kasashen duniya na suka da babbar murya kan batun zubar da ruwan dagwalon nukiliyar cikin teku, sai dai gwamnatin kasar ta gaza gano laifinta, tana wasan kalmomi domin yaudarar al’ummun kasa da kasa, tare kuma da dora laifin kan sauran kasashe. Cikin takardun da kafofin watsa labarai da gwamnatin kasar Japan suka fitar, an yi amfani da kalmomin “ruwan dagwalon nukiliya”, amma ma’aikatar harkokin wajen kasar tana amfani da kalmomin “ruwan nukiliyar da aka sarrafa wato ALPS”.

Sai dai, karyar kasar Japan ba za ta iya yaudarar al’ummun kasa da kasa ba. Kamar yadda wasu masana suka bayyana, ruwan dagwalon cibiyar sarrafa sinadarin nukiliya dake Fukushima yana cike da sinadarai masu hadari da dama, bayan aukuwar hadarin nukiliya a cibiyar. Akwai bambancin tsakanin ruwan dagwalon nukiliyar cibiyar sarrafa sinadari dake Fukushima da ruwan nukiliyar da aka sarrafa a cikin tasoshin samar da lantarki daga karfin nukiliya, domin ba su taba haifar da hadari ba. Ya kamata kasar Japan ta ji kunyar yaudarar al’ummun kasa da kasa.(Jamila)