logo

HAUSA

Ya kamata Amurka ta riga sauran kasashen duniya gudanar da binciken asalin annobar COVID-19

2021-05-28 14:21:22 CRI

A ran 26 ga watan, shugaban kasar Amurka Joe Biden, ya umarci hukumar lekan asiri ta kasarsa, da ta binciki asalin dalilin da ya haddasa annobar COVID-19, don gano ko ta fito ne daga halittu ko dakin gwaji. Ya kuma nemi hukumar lekan asiri da ta gabatar da wani rahoto cikin kwanaki 90 masu zuwa. Har ma Joe Biden ya ce, kasar Amurka za ta ci gaba da yin hadin gwiwa da kawayenta, domin ganin kasar Sin ta gudanar da bincike irin na kasa da kasa. Yanzu ga wani cikakken bayani mai lakabi “Ya kamata Amurka ta riga sauran kasashen duniya gudanar da binciken asalin annobar COVID-19” da abokin aikinmu Sanusi ya hada mana.

Batun neman asalin dalilin da ya haddasa annobar, batu ne na kimiyya, don haka abun tambaya shi ne me ya sa hukumar leken asiri ce za ta yi binciken? Sannan an riga an gama aikin binciken a kasar Sin, mene ne kuma zai sa a yanzu shugaban ke son ci gaba da “neman” kasar Sin ta sake yin wani binciken?

Ya kamata Amurka ta riga sauran kasashen duniya gudanar da binciken asalin annobar COVID-19_fororder_210528-rahoto-Sanusi-hoto1

A fili ne gwamnatin kasar Amurka mai ci tana son siyasantar da batun annobar ne kawai. Kamar yadda yau shekaru 20 da suka gabata, gwamnatin Jr. Bush ta Amurka, ta nemi hukumar lekan asiri da ta binciko abubuwan da za su iya shaida cewa, wai kasar Iraki ta samar da makaman kare dangi a babban mataki. Hakikanan wadannan abubuwa sun shaida cewa, gwamnatin Amurka tana yin irin wannan bincike ne domin a zukatan ’yan siyasan kasar Amurka, “ana da laifi”.

Sanin kowa ne, a cikin wani rahoto da tawagar kwararrun kiwon lafiya ta kasa da kasa ta hukumar kiwon lafiya ta kasa da kasa, wato WHO ta gabatar a karshen watan Maris na bana, an riga an tabbatar da cewa, “ba zai yiwu ko kadan” kwayoyin cutar numfashi ta COVID-19 su yi yoyo daga dakin gwaji ba.

Matakin siyasantar da batun da gwamnatin Biden ta dauka, ya bayyana cewa, wasu Amurkawa ba su koyi darasi ko kadan ba, maimakon haka a yanzu suna gudu cikin sauri a kan hanyar yakar ilmin kimiyya, bisa radinsu na son kai, da kuma rashin hangen nesa. Sakamakon haka, suna kawo cikas ga yunkurin yakar annobar da sauran sassan duniya suke yi.

Idan kasar Amurka ta dinga tsayawa matsayinta, cewa wai kwayoyin cutar sun yi yoyo ne daga dakin gwaji, to, dole ne a fara bincike kan dakunan gwaje-gwaje na kasar Amurka, wadanda suke cikin kasar Amurka da sauran sassan duniya.

Ya kamata Amurka ta riga sauran kasashen duniya gudanar da binciken asalin annobar COVID-19_fororder_210528-rahoto-Sanusi-hoto2

A watan Maris na bara, Mr. Robert Redfield, tsohon shugaban cibiyar kandagarkin cututtuka ta kasar Amurka ya amince da cewa, a hakika dai wasu daga cikin wadanda suka mutu sakamakon cutar mura a watan Satumban shekarar 2019, sun mutu ne sakamakon cutar COVID-19. Amma kuma har yanzu ba a san daidai lokacin da Ba’amurke na farko ya kamu da cutar COVID-19 ba. Idan ana son samun amsar wannan tambaya, abin da ya fi muhimmanci shi ne a yi bincike a kasar Amurka yanzu.

Bugu da kari, ana da tambayoyi da dama game da dakunan gwaje-gwajen halittu na kasar Amurka, wadanda suke cikin kasar, da kuma na wasu sauran sassan duniya. Alal misali, a watan Yulin shekarar 2019, ba zato ba tsammani, kasar Amurka ta rufe dakin gwajin halittu na Fort Detrick dake jihar Maryland ta kasar Amurka. Tun lokacin rufe shi, har zuwa yanzu ba a san dalili ba. Kuma wata cutar sigari irin ta lantarki ta bulla a wata unguwa dake jihar Virginia. Alamomin duk wanda ya kamu da cutar sun yi kusan daidai matuka, da na wadanda suke kamuwa da cutar COVID-19. Shin bai kamata a yi bincike kan irin wannan tambayar da ake da ita ba, a lokacin da ake binciken asalin dalilin da ya haddasa cutar?

Dole ne a yi binciken asalin dalilin da ya haddasa cutar bisa ilmin kimiyya, kuma bai kamata a siyasantar da lamarin ba. Tabbas ne cutar za ta hukunta duk wanda ya saba da wannan ka’ida. Hakikanan abubuwan da suka faru a cikin shekara 1 ko fiye da suka gabata, sun riga sun shaida hakan. Kuma ko ’yan siyasan kasar Amurka suna son ci gaba da aikata irin wannan laifi? Yanzu suna cacar baki ne kadai, don haka me ya sa ba su iya daukar wasu matakai masu amfani, domin bayar da gudummawarsu wajen dakile cutar?

A gaban wannan muhimmin batu, bai dace wasu Amurkawa su mayar da baki fari, ko dora laifi kan wani ba. Muna son sanin shin a yaushe kasar Amurka za ta iya gayyatar kwararrun kiwon lafiya na WHO, don su yi cikakken bincike a kasar Amurka kamar yadda kasar Sin ta yi? Yaushe kasar Amurka za ta amsa wannan tambaya ga duk duniya baki daya? (Sanusi Chen)