logo

HAUSA

Al’ummun kasa da kasa suna juyayin rasuwar Yuan Longping

2021-05-24 19:42:33 CRI

Al’ummun kasa da kasa suna juyayin rasuwar Yuan Longping_fororder_Yuan Longping

Yau Litinin 24 ga wata, an shirya bikin ban kwana da gawar Yuan Longping, masanin aikin gonan kasar Sin, wanda ake kiran sa “mahaifin tagwaita irin shinkafa” a birnin Changsha, fadar mulkin lardin Hunan dake kudancin kasar Sin.

Tun bayan rasuwarsa a ranar 22 ga wata, hukumomin kasa da kasa da dama, ciki har da MDD, da hukumomin gwamnatocin kasashen duniya daban daban, da kafofin watsa labarai, da masu amfani da kafar Intanet a fadin duniya, sun rubuta bayanai domin nuna juyayi mai zurfi ga rasuwarsa.

A shekarun 1970, adadin shinkafar da aka noma ta hanyar amfani da fasahar tagwaita irin shinkafa a kasar Sin, ya haura na yau da kullum da kaso 20 bisa dari. Wato karin shinkafar da aka samu ta ciyar da karin mutane miliyan 70 a ko wace shekara.

Ya zuwa farkon shekarun 1990, hukumar abinci da aikin gona ta MDD wato FAO, ta mayar da aikin yada fasahar tagwaita irin shinkafa a matsayin matakin farko wajen daidaita matsalar karancin abinci a kasashe masu tasowa. Haka kuma ta gayyaci dattijo Yuan Longping, da ya kasance babbar mai ba da shawara na kasa da kasa a bangaren. Alkaluman da aka samar sun nuna cewa, a cikin gomman shekarun da suka gabata, adadin masanan fasahar tagwaita irin shinkafa na kasashe masu tasowa sama da 80 da Yuan Longping ya horas da su, ya kai sama da 14,000.

Yanzu haka ana noma irin shinkafa da aka tagwaita a kasashen Indiya, da Vietnam, da Amurka, da Brazil da kasashen Afirka, kuma matsakaicin adadin irin shinkafar da aka tagwaitar da ake samu a ko wace kadada, ya fi adadin shinkafa mai inganci da ake samu a gona mai fadin kadada daya yawa, wanda kan kai har tan biyu. A Madagascar, inda al’ummun kasar da yawansu ya kai miliyan biyu suka taba fama da yunwa, an buga hoton tagwaita irin shinkafa a kan takardar kudin kasar.

Bayan kokarin da suka yi a cikin gomman shekarun da suka wuce, Yuan Longping da tawagar masanan aikin gonan dake karkashin jagorancinsa, sun tabbatar da samar da isasshen abinci, haka kuma sun rage karancin abinci da talauci a fadin duniya, har ma sun taka rawar gani wajen kiyaye zaman lafiyar duniya.

Labaran Sinawa wadanda suke kokarin kyautata rayuwar al’ummun kasa da kasa sun shaida cewa, kasar Sin na kasancewa jigon samun ci gaba kuma abokiyar huldar kasashen duniya a ko da yaushe.  (Jamila)