logo

HAUSA

Ya kamata Amurka ta cika alkawarinta a zahiri

2021-05-12 15:47:30 CRI

Ya kamata Amurka ta cika alkawarinta a zahiri_fororder_hoto

Kwanan baya, gwamnatin kasar Amurka ta nuna goyon baya kan ba da kariya game da ’yancin mallakar fasahar samar da alluran rigakafin cutar COVID-19 daga dokar ’yancin mallakar fasaha. Dangane da wannan batu, jaridar The Washington Post ta kasar Amurka ta wallafa wani sharhin dake cewa, matakin gurguwar dabara ce, a kokarin da ake na sassauta yanayin yaduwar annobar, amma, wannan mataki na Amurka, ya janyo hankulan ’yan kasar, musamman ma, masu kada kuri’a. Wasu na ganin cewa, gwamnatin kasar Amurka ta nuna ra’ayinta ba tare da la’akari abin da zai biyo baya ba, domin wannan buri, wani mataki ne na cimma moriya ta siyasa.

Sanin kowa ne cewa, idan har aka ba da kariya game da ’yancin fasahar samar da alluran rigakafin cutar COVID-19, ya kamata matakin ya samu amincewar dukkan mambobin kungiyar WTO 164. Haka kuma, idan ana son cimma wannan buri, wajibi ne, mambobin kungiyar WTO, su yi shawarwari kan batun. Wannan lamarin ba zai taimaka wajen yaki da annobar cutar COVID-19 ba. Shi ya sa, shugabar kungiyar tarayyar kasashen Turai Ursula von der Leyen ta ce, babban aikin dake gabanmu a halin yanzu, shi ne, samar da isassun alluran rigakafi ga al’ummomin kasashen duniya cikin adalci, a maimakon bata lokuta wajen yin tattaunawa kan ko za a ba da kariya game da ’yancin mallakar fasahar samar da alluran rigakafin cutar COVID-19 daga dokar ikon mallakar fasaha.

Kuma, a halin yanzu, dalilin da ya haddasa matsalar alluran rigakafi shi ne raba allura cikin yanayin na rashin adalci. Gwamnatin kasar Amurka ta hana kamfanonin kasarta fitar da alluran rigakafi zuwa kasashen ketare, lamarin da ya sa, ta boye alluran rigakafi fiye da adadin da take bukata, yayin da wasu kasashe suke fama da matsalar karancin alluran rigakafi mai tsanani. Kuma, abu mafi bata ran al’umma shi ne, kasar Amurka ta hana fitar da kayayyakin da ake bukata wajen hada alluran rigakafin COVID-19 zuwa kasashen ketare, lamarin da ke kawo cikas ga hadin gwiwar kasashen duniya a fannin yaki da wannan annoba. A don haka, wasu na ganin cewa, “Amurka ta kan furka kamalai kamar wata mai ladabi, amma, a zahiri ladabin kura ne!” (Mai Fassarawa: Maryam Yang)