logo

HAUSA

Jam’iyyar JKS Tana Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Hada Kan Al’Ummar Sinawa Baki Daya

2021-05-05 17:46:08 CRI

图片默认标题_fororder_BE6F0FFA-670E-4181-9CDF-E4144270E619

Kwanan baya, jerin wasu shirye-shiryen bidiyoyi sun yi suna matuka a yanar gizo, a nan kasar Sin da waje. Cikin shirye-shiryen bidiyoyin masu lakabin “Ni jama’a ce”, masu kunshe da wasu labarai dangane da mutane masu hazaka a nan kasar Sin, akwai wani babi mai suna “Tinkarar mawuyacin hali”, wanda ya bayyana labarin Zhao Zhiquan, mamallakin wani kamfani mai zaman kansa. 

Zhao Zhiquan ya yi iyakacin kokarin taimakawa mutane masu karancin kudin shiga dake fama da ciwon zuriya, kuma domin neman fitar da kamfaninsa daga mawuyacin hali, ya jagoranci ma’aikantansa, inda suka kwashe shekaru fiye da 27 suna kokarin nazarin magunguna, matakin da ya sauya kamfanin daga karamin kamfani da ya kusan durkushewa, zuwa babban rukunin samar da magunguna a duniya, matakin da ya kuma samar da gudummawar bunkasa tattalin arzikin wurin. 

Har kullum, Zhao Zhiquan kan ce, “Burin kafa kamfani shi ne amfanawa al’umma, tare da samarwa ma’aikatansa rayuwa mai kyau”. 

Kafin rasuwarsa, bai mika gadon kamfaninsa ga danginsa ba, saboda fatan sa shi ne wani dake da karfin tallafawa al’umma ya samu ikon mallakar kamfanin na sa.

Masu kallon shirye-shiryen ‘yan kasashen ketare sun yi matukar mamaki, har wanin su ya ce; “Ina mamaki matuka bisa yadda wani mai kamfani ya iya bautawa al’ummar kasarsa kamar haka.” Wani kuma ya ce, “Wannan bidiyo ya kara mana kwarin gwiwa, ina jinjinawa abin da mai kamfanin nan na kasar Sin ya yi.”

To amma ko me ya sa masu kamfani kamar Zhao Zhiquan ke iya bautawa kasar su, da al’ummarsu, a maimakon neman cin riba kawai? Kuma me ya sa kamfanin Zhao Zhiquan ya iya samun ci gaba irin wannan?

Lalle dalili shi ne Zhao Zhiquan shi ba shugaban wannan kamfani ba ne kawai, a daya bangaren ya kuma kasance sakataren reshen jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin a waccan lokaci. Kana mamban jam’iyyar JKS ba sa ja da baya, yayin da suke fuskantar kalubaloli da mawuyancin hali. Suna sauke nauyin dake wuyansu na jagorantar jama’a, a yayin da ake tunkarar mawuyancin hali.

Daidai a sakamakon yadda Mambobin JKS irinsu Zhao Zhiquan ke jagorantar jama’a a fannin samar da damammakin bunkasuwar tattalin arziki, ya ke hada kan jama’a baki daya, wajen tinkarar mawuyancin hali, da samun bunkasuwa da wadata tare.

Amma, kokarin jama’a kawai, ba ya iya samar da ci gaba kamar na kamfanin Zhao Zhiquan. Idan an waiwayi tarihin bunkasuwar kamfanoni masu zaman kansu na kasar Sin, ana iya ganin cewa, jam’iyyar JKS da gwamnatin kasar Sin, su kan baiwa kamfanoni taimako ko da yaushe.

A gun taron tattaunawa da ya yi tare da masu kamfanoni masu zaman kansu a shekarar 2018, babban sakataren jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, Xi Jinping ya bayyana cewa, “Kamata ya yi gwamnati ta samar da yanayi mai kyau ga bunkasuwar kamfanoni masu zaman kansu, da taimaka musu wajen tinkarar mawuyancin hali, da nuna musu goyon baya, ta yadda za su kara karfin kirkire-kirkire, da samun bunkasuwa yadda ya kamata.” Furucin da ya baiwa kamfanonin masu zaman kansu kwarin gwiwa, da samar musu alkibla mai kyau.

A karkashin nagartattun manufofin jam’iyyar JKS, da ma jagorancin mambobinta, kamfanoni masu zaman kansu sun daukaka, sun kuma samu karfi, har sun fitar da rassan su kasashen waje. Ya zuwa yanzu, yawan kamfanoni masu zaman kansu ya kai kaso 90% na dukkan kamfanonin kasar, kuma yawan guraben aikin yi da suka samar ya kai fiye da 80%. Kaza lika yawan haraji da suka biya ya kai sama da kaso 50%, inda yawan GDP da suka samar ya kai fiye da 60%, kuma yawan kirkire-kirkire da suka samar ya wuce kaso 70%. 

Daga cikin kamfanoni mafi karfi dake sahun gaba a duniya su 500, yawan kamfanoni masu zaman kansu na kasar Sin ma ya karu, zuwa 28 a shekarar 2018, daga 1 kacal a shekarar 2010.

Mafarkin al’ummar kasar Sin, shi ne Sinawa baki daya su samu wadata. Al’ummar kasar na yin iyakacin kokarin cimma wannan muradu, a yayin da gwamnatin kasar ke mara musu baya. A karkashin goyon baya mai inganci da jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin da gwamnatinta suke ba su, jama’ar kasar Sin na iya hada karfin da karfe don cimma muradu tare. Hakan kuwa, ya yi daidai da bayanin da dakta Agaba Halidu, mai nazarin harkokin siyasa da huldar kasa da kasa na jami’ar Abuja ya wallafa a jaridar Blue Print, a kwanan baya, inda ya ce jam’iyyar JKS tana taka muhimmiyar rawa, wajen hada kan al’ummar Sinawa baki daya, matakin da ke taimakawa wajen ingiza bunkasuwar tattalin arziki, da zamantakewar al’ummar kasar ta Sin. (Amina Xu)