logo

HAUSA

Kungiyar G7: Mai Dokar Bacci Ya Bige Da Gyangyadi

2021-05-04 18:41:04 CRI

Kungiyar G7: Mai Dokar Bacci Ya Bige Da Gyangyadi_fororder_210504-Sharhi-Faeza-hoto

A yau Talata ne Birtaniya za ta karbi bakuncin taron ministocin harkokin wajen kasashe 7 masu karfin tattalin arziki a duniya wato G7, inda wannan zai zama karo na farko da ministocin za su gana ido da ido, tun bayan bullar cutar COVID-19 a duniya.

Birtaniya ce ke rikon shugabancin karba-karba na kungiyar da ta kunshi kasashen Amurka da Faransa da Jamus da Canada da Japan da kuma Italiya. Inda a wannan taro kuma, aka gayyaci wakilai daga kasashen Australia da Afrika ta Kudu da Korea ta Kudu da India da Brunei da kuma Tarayyar Turai don su halarci taron.

A cewar ministan harkokin wajen Birtaniya, tattaunawar za ta ba su damar zama tare domin tunkarar manyan kalubalen dake ci musu tuwo a kwarya. Kuma a cikin batutuwan da suka fi mayar da hankali ciki, akwai batun da ya shafi kasar Sin da Rasha da sauran wasu batutuwan kasa da kasa.

A lokacin da duniya ke cikin wani mawuyacin hali, na matsalolin tattalin arziki da zamantakewa da cutar COVID-19 ta haifar, da ma uwa uba kokarin dakile annobar dake ci gaba da cin karenta babu babbaka, wadannan manyan kasashe na mayar da hankali kan batutuwan cikin gidan kasashe kamar na Sin da ko kadan bai shafe su ba.

Duk da cewa bayan tattaunawar da aka yi jiya Litinin tsakanin sakataren harokokin wajen Amurka Anthony Blinken da takwaransa na Birtaniya Dominic Rabb, Blinken din ya ce ba su da niyyar dakilewa ko durkusar da kasar Sin, sai dai kokarin daukaka dokoki da ka’idojin duniya domin kasashensu sun yi namijin kokari wajen kiyaye dokokin tsawon gomman shekaru.  Sai dai a bayyane yake cewa, matakan da Amurka ke dauka da kuma irin furucin jami’anta sun sha bamban. Yaushe ne yin katsalandan da tsoma baki cikin harkokin gidan wasu kasashe ya zama daukaka ka’idoji da dokokin duniya? Yaushe ne zagon kasa da yada jita-jita da kokarin rura wutar rikici tsakanin al’ummar dake zaune lafiya ya zama kiyaye ka’idojin duniya? Hakika babu abun da wadannan manyan kasashe ke yi illa abun da ake kira da “laifi tudu ne, ka hau naka ka hango na wasu”, wato Amurka sam ba ta ganin laifinta, sai dai kokarin kirkiro laifi a inda babu, saboda wasu moriyarta na kashin kai.

Haka kuma, kasashen na batun daukaka huldar kasa da kasa wanda sam ba haka yake a aikace ba, don kuwa an ga yadda Amurka ta janye daga yarjeniyoyin kasa da kasa da yadda take gaban kanta wajen kakaba takunkumi har ma da yadda ita da kawayenta ke zartas da dokoki kan harkokin gidan kasashe.

Baya ga haka, za su tabo batun rabon riga kafi COVID-19 cikin adalci. Tun bayan fara amfani da riga kafin, wadannan kasashe da suke ikirarin manya ne, ba su yi hobbasa wajen taimakawa al’ummomin duniya masu rangwamen gata ba, sai ma suka mayar da hankali wajen saye rigakafin dake akwai, har ma suke sayensa fiye da kima, wanda ya nuna ainihin halayyarsu ta son kai. Misali na baya-bayan nan shi ne, yanayin da Indiya ta tsinci kanta a ciki. Duk da huldar dake tsakanin India da Amurka da Birtaniya, kasar Sin ta riga su kai mata dauki. Duk kuwa da irin takalarta da Indiyar ke yi, Sin ta nuna cewa ita din babbar kasa ce mai sanin ya kamata. Amma Amurka sai tsayawa ta yi da alkawarin fatar baki, tana cewa, kulawa da al’ummarta ce a kan gaba.

Ya kamata kasashen nan su lura cewa, duniyar nan a dunkule take, kuma makomar dukkan al’ummarta na hade da juna. Babu yadda za a yi a ce zaman lafiya da wadata ta wanzu a duniya muddun ba su sauya salonsu ba. Ya kamata su lalubo hanyoyin lumana na warware sabaninsu da kasashen da suke dauka a matsayin barazana, kuma ya kamata a kyale kowacce kasa ta rungumi dabara ko salon shugabanci da ya dace da ita. Babakere ko fin karfi da cin zali, ba zai taba kai mu ga samun duniyar da muke muradi ba. (Fa’iza Muhammad Mustapha)