logo

HAUSA

Yadda Sin take taimakawa India ya nuna al’adunta na son zaman jituwa

2021-05-03 17:12:25 CRI

Yadda Sin take taimakawa India ya nuna al’adunta na son zaman jituwa_fororder_20210503-sharhi-Bello

A kwanakin nan, tsanantar yanayin annobar COVID-19 a kasar India ta janyo hankalin mutanen kasashe daban daban. Dangane da batun, kasar Sin, a matsayin wata babbar kasa, ta sauke nauyin da ke wuyanta, inda ma’aikatar harkokin wajen kasar ta bayyana niyyarta ta taimakawa kasar India har karo 7, yayin da wasu kasashen yammacin duniya irinsu Amurka da Birtaniya suka ce za su yi kokarin biyan bukatun cikin gidansu da farko, inda suka yi tsumulmular tura wasu kayayyakin dakile cutar COVID-19 ga kasar India.

Wani abun da ya kamata a lura da shi game da huldar dake tsakanin Sin da India, shi ne sojojin kasar India sun taba kutsa kai cikin harabar kasar Sin a watan Yunin bara a kwarin Gallevan dake kan iyakar kasashen biyu, tare da ta da rikici da sojojin kasar Sin, lamarin da ya haddasa rasuwar sojojin kasar Sin 4. Bayan wannan kuma, kasar India ta dauki wasu matakai na kayyade jarin kamfanonin kasar Sin dake India, tare da sanya su shan asara sosai. Kana yadda kasar India take kallon kasar Sin a matsayin wadda ke takara da ita, ya sa ta waswasin ko za ta karbi tallafin da kasar Sin ta samar ko a’a.

Sai dai duk da haka, kasar Sin ta riga ta cika alkawarin da ta yi na tallafawa kasar India. A cewar Sun Weidong, jakadan kasar Sin dake kasar India, tun daga farkon watan Afrilun bana, kasar Sin ta riga ta samar da na’urorin taimakawa numfashi fiye da 5000, da injunan samar da isakar Oxygen 21569, da marufin baki da hanci fiye da miliyan 21.48, gami da magungunan da nauyinsu ya kai kimanin ton 3800, ga bangaren India. A sa’i daya kuma, kamfanonin kasar Sin masu hada na’urorin aikin jinya suna kokarin samar da kayayyaki ba dare ba rana, don biyan bukatun jama’ar kasar India.

To me ya sa kasar Sin take da karamci kamar haka?

Saboda kasar Sin ta san cewa, idan an bar yanayin cutar COVId-19 ya ci gaba da tsananta a kasar India, to, annobar ka iya kara yaduwa zuwa kasashe makwabta, har ma da sauran kasashe daban daban na duniyar mu. Ban da wannan kuma, wani babban dalilin da ya sa kasar Sin ta iya hakuri da wasu abubuwan da kasar India ta yi mata a baya, gami da taimakawa kasar a wannan lokacin da take da bukata, shi ne domin al’adun musamman na kasar na neman zaman jituwa da sauran kasashe.

A yayin bikin kaddamar da wasannin Olympics na birnin Beijing na kasar Sin a shekarar 2008, Sinawa sun taba nuna kalmar “zaman jituwa” a tsakiyar wani babban filin wasa, don nuna wa mutanen duniya wani babban jigo na al’adun kasar, wato “zama cikin jituwa tare da sauran sassan duniya”. Shugaban kasar Sin Xi Jinping, wanda ke kaunar al’adun gargajiyar kasarsa, ya taba bayyana al’adun “zaman jituwa” na kasar Sin kamar haka: Sinawa suna jituwa tare da sauran al’ummomi, gami da muhallin duniyarmu, inda suke neman zama cikin jituwa tare da mutanen da suke da mabambantan ra’ayoyi, da aikata alheri da abubuwan kirki. Wannan al’adu na musamman ya sa kasar Sin gabatar da shawarar kafa “al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makoma ta bai daya” a duniya.

Ban da taimakawa India, akwai sauran misalan tasirin al’adun neman jituwa na kasar Sin kan manufofin kasar. Misali, a ranar 29 ga watan Afrilu, kasar Sin ta yi nasarar harba wani muhimmin bangare na tashar binciken sararin samaniya ta kasar, wanda takensa shi ne “ Tian He”, wanda ke nufin: Neman samun jituwa a sararin samaniya. Yadda kasashen yammacin duniya suke haramta samar da bayanan kimiyya da fasaha ga kasar Sin, ya tilastawa kasar dogaro kan masu nazarin kimiyya da fasaha na kasarta wajen tsara fasahohin binciken sararin samaniya. Duk da haka, kasar Sin ta kebe wurare domin saukar da masu nazarin kimiyya da fasaha na kasashe daban daban, a cikin sabuwar tashar binciken sararin samaniya da take kokarin hadawa. A watan Yunin shekarar 2019, kasar Sin ta riga ta sanar da cewa, an baiwa kasashe 17 da ayyukan bincikensu guda 9, damar shiga tashar binciken sararin samaniya ta kasar a jerin farko.

Kafin wannan kuma, a yayin taron koli na batun yanayi da aka kira a ranar 22 ga watan Afrilu, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da wani jawabi mai taken “Kafa wata al’ummar bai daya da ta shafi dan Adam da muhallin duniya”, inda ya nuna al’adun Sin na neman jituwa sosai. A cewar shugaba Xi, Sinawa na son samun jituwa tsakanin dan Adam da muhallin duniya, kana kasar Sin na kira ga kasashe daban daban, da su kara kokarin hadin gwiwa da juna, maimakon dora wa juna laifi, da kokarin cika alkawari, don samar da gudunmowa tare ga yunkurin daidaita muhallin duniya.

Hakika kasashe tamkar mutane ne, kowanensu na da wata halayyar musamman. Wasu kasashe, kamar kasar Sin, suna son samun jituwa da saura kasashe, inda suke kokarin yayata ra’ayin kasancewar bangarori masu fada a ji daban daban a duniya, da kokarin hadin kai don amfanawa juna. Kana wasu kasashe, a nasu bangare, ba sa hangen nesa, inda maimakon neman jituwa da sauran kasashe, suke kokarin ta da rikici tsakaninsu da sauran kasashe. Dangane da wannan batu, Sinawa su kan ce, “Ta hanyar yin hadin gwiwa, za a amfanawa juna, yayin da rikici zai lahanta moriyar kowa.” Kana kasar Sin ta kan yi kokarin daukar wasu matakai na tabbatar da jituwa a duniya, don nuna wa wadannan kasashe cewa, neman jituwa,maimakon ta da rikici, hanya ce da ta fi dacewa da moriyar kasashen duniya. (Bello Wang)

Bello