logo

HAUSA

Koguna na komawa yadda suka kasance a baya a garinmu

2021-04-30 23:36:47 CRI

Koguna na komawa yadda suka kasance a baya a garinmu_fororder_微信图片_20210430232054

Kwanan nan, na koma garinmu Kunming don haduwa da iyalaina a lokacin hutu. Kunming babban birni ne na lardin Yunnan, wanda ke kudu maso yammacin kasar Sin.

Ni da iyalaina mun je kogin Panlong don shakatawa, kogin da mazauna birnin Kunming ke dauka a matsayin mahaifiya, wanda daga arewa zuwa kudu, ya ratsa birnin baki daya. Kogin yana ta malala, kuma mazauna birnin da yawa suna zuwa wajen sa domin shakatawa, bisa irin kyakkyawan yanayin kogin.

Lokacin da muke tsaye a gabar kogin, mahaifina yana kallon kogin ya ce, “Kogin kusan ya koma yadda yake a lokacin da nake karami.”

Koguna na komawa yadda suka kasance a baya a garinmu_fororder_微信图片_20210430232108

An haifi mahaifina a shekarun 1950, kuma tsohon gidan kakana yana gabar kogin, don haka mahaifina ya girma ne a kusa da kogin. Ya tuna da cewa, a lokacin, ruwan kogin yana da inganci sosai, har ana iya ganin kasansa, kuma mazauna gabobin kogin suna debo ruwa daga kogin a kowace rana, domin bukatun yau da kullum. Kowace rana da sassafe, su kan debo ruwan sha daga kogin su koma gida su zuba cikin tukunya. Daga baya, bi da bi su kan koma kogin don wanke tufafi da sauransu. Mahaifina ya ce, abin da ya fi faranta masa rai a lokacin shi ne, samun damar iyo a cikin kogin a lokacin zafi.

Sai dai a sakamakon karuwar al’umma da bunkasuwar masana’antu, da ma yadda jama’a suka gaza fahimtar muhimmancin kiyaye muhalli, da ma rasa daukar ingantattun matakai, an zuba gurbataccen ruwa da yawa da aka fitar daga rayuwar yau da kullum, da na masana’antu cikin kogin, don haka ruwan kogin ya gurbata. Mahaifina ya ce, “Ban iya tabbatar da takamaimen lokacin da ruwan kogin ya fara gurbata ba, sai dai sannu a hankali ne ruwan ya zama gurbatacce, har ma daga karshe ya zama baki kirin.”Jama’ar da ke wucewa ta wurin kogin, dole sai su rufe baki da hanci sabo da warrinsa, balle ma a ce za a ci gaba da debo ruwan kogin, domin amfani na rayuwar yau da kullum.

Koguna na komawa yadda suka kasance a baya a garinmu_fororder_微信图片_20210430232132

Abin da ya fi bakanta wa mazauna birnin rai shi ne tabkin Dianchi, wanda suke dauka a matsayin uwarsu ma ya gurbata. Dianchi ya kasance tabki mai ruwa marar gishiri mafi girma na shida a kasar Sin, wanda kuma ya zama mafi fadi a lardin Yunnan. Tabki ne da mazauna birnin ke alfahari da shi. Tabkin yana da nisan kilomita sama da 10 daga cibiyar birnin Kunming, kuma kogin Panlong ya malala kafin daga bisani ya shiga cikin tabkin Dianchi, wanda ya kasance kogi mafi girma da ya shiga cikin tabkin.

Har yanzu ina iya tunawa da yadda malaminmu na makarantar midil ya bayyana mana tabkin Dianchi, ya ce,“A lokacin da nake karami, mu kan shiga kwale kwale a karshen mako don mu shakata a tabkin Dianchi. A lokacin da rana ta haskaka tabkin, har muna iya ganin kasan tabkin, Ottelia acuminata masu fararen furanni ne, kuma suna rayuwa cikin tabkin. Sai dai abin bakin ciki shi ne, yanzu ba ku iya ganin hakan.”

Ottelia acuminata nau’in tsirrai ne da ake samu a koguna da tabkuna na kasar Sin, wandanda ba sa iya rayuwa idan ba a cikin ruwa mai inganci sosai ba. A yayin da ruwan tabkin Dianchi ya gurbata, nau’in tsirran ma ya bace kwata kwata daga tabkin.

Koguna na komawa yadda suka kasance a baya a garinmu_fororder_微信图片_20210430232123

Daga nan, jama’a sun fara gane muhimmancin kiyaye muhalli. A shekarun 1990, an fara daukar kwararan matakai na daidaita matsalar gurbacewar tabkin Dianchi, aikin da aka dinga sakawa cikin shirye-shiryen raya kasar Sin na shekaru biyar biyar.

Mahaifina ya ce, “A baya, ba mu fahimci muhimmancin kiyaye muhalli sosai ba, abin da ya haddasa mana munanan hasarori. A cikin ‘yan shekarun baya, shugaban kasarmu Xi Jinping ya gabatar da cewa, kiyaye muhalli shi ne tushen bunkasuwar tattalin arziki, wanda ya sa muka gane cewa, ba sai mun gurbata muhalli ba za mu iya bunkasa tattalin arzikinmu. A hakika, ingantaccen muhalli ma zai taimaka ga bunkasa tattalin arziki.”

Rahoton da aka gabatar a gun taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18, wanda ya gudana a shekarar 2012 ya nuna cewa, ya zama dole a sanya aikin kiyaye muhalli a wani muhimmin matsayi. Baya ga haka, taron ya kuma zartas da gyararren tsarin dokokin jam’iyyar, inda aka saka “jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ta zama mai jagorantar jama’ar kasar wajen gina kasa mai ingantaccen muhalli” a ciki. Tabbas, yadda wata jam’iyyar siyasa musamman ma jam’iyyar da ke kan karagar mulki ya sanya aikin kiyaye muhalli cikin tsarin dokokinta, jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ta zama ta farko a duniya.

“Da ma tabkin Dianchi abun alfahari ne ga jama’ar Yunnan, musamman na jama’ar Kunming, amma ga shi yanzu ya zama abin kunyarsu, gaskiya wannan babbar hasara ce. Dole ne a dukufa a kan daidaita yanayin tabkin Dianchi, da Erhai, da Fuxianhu da dai sauran tabkuna.” Shugaban kasar Sin, kana babban sakataren jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, Mr.Xi Jinping ya fadi haka a lokacin da ya yi rangadi a lardin Yunnan a watan Janairun shekarar 2015.

Koguna na komawa yadda suka kasance a baya a garinmu_fororder_微信图片_20210430232140

Kwalliya ta biya kudin sabulu. Bisa namijin kokarin da aka yi, ruwan koguna 35 da ke shiga tabkin Dianchi, da ma ruwan tabkin Dianchi baki daya ya yi ta inganta, daga matsayin da bai kai V ba, har zuwa na Ⅲ a bara. A yayin da yanayin tabkin Dianchi ya ke ta kyautata, nau’o’in halittun da ake gani a wurin ma sun karu sosai.

Yanzu haka, da tabkin Dianchi, da kogin Panlong, da ma sauran koguna suna komawa yadda suka kasance a baya, suna kuma jawo hankulan dimbin mazauna birnin zuwa wurin domin shakatawa. Baya ga kuma baki na gida da kuma na waje. Kwanan baya, akwai labarin da ke cewa, an gano Ottelia acuminata a wasu sassan na tabkin Dianchi. Lallai na yi farin ciki, a ganina, nan ba da jimawa ba,zan iya gani da ido na, yadda tabkin Dianchi, da kogin Panlong suka kasance a lokacin da mahaifina ke karami.

Fata na kuma shi ne, zuriyoyinmu ma za su iya ci gaba da ganin kyakkyawan yanayinsu.(Lubabatu)