logo

HAUSA

Girma Ya Fadi

2021-04-28 17:11:15 CRI

Girma Ya Fadi_fororder_1219-2

A yayin da kasashen duniya irinsu kasar Sin ke rabawa tare da sayar da alluran riga kafin annobar COVID-19 da suka samar ga kasashe mabukata da kawayensu, ita kuma Amurka dake zama babbar kasa a duniya, tana boye riga kafin ne, maimakon ta taimakawa kasashe masu bukata ko ma ta yiwa al’ummominta alluran riga kafin.

Wannan mataki da mahukuntan kasar Amurka suka dauka, ya sa jama’a bayyana fushi da suka ta kafofin sada zumunta, kan yadda Amurkar da ma kasashen yammacin duniya suke boye alluran riga kafin COVID-19, matakin da kowa ke cewa gurguwar shawara ce, wadda ba za ta kai kasar ga gaci ba.

Hukumar lafiya ta duniya (WHO), ta sha yin kira ga manyan kasashe da ma kamfanonin dake samar da alluran riga kafin annobar, da su raba su bisa adalci da sauran kasashe, musamman kasashe masu tasowa. Wannan ne ma ya sa MDD take jagorantar shirin nan na COVAX, mai raba riga kafin ga kasashe bisa daidaito da adalci, musamman kasashe masu tasowa.

Masu fashin bakin dai, sun yaba kokarin kasar Sin, bisa cika alkawatin da ta yi tun farko cewa, da zarar ta gudanar da bincike ta kuma samar da riga kafin, to zai kasance hajar al’ummar duniya.

Wannan gurguwar shawara da Amurka ta dauka na boye riga kafin, ba zai kasance mai fa’ida ga hadin gwiwar kasa da kasa kan yaki da wannan annoba ba. Yanzu haka, annobar ta sake bulla a karo na uku a kasar Indiya, inda take ci gaba da hallaka rayukan jama’a, baya ga sauran kasashe dake fama da wannan annoba.

Wani rahoto da jaridar Times of India (TOI) ta wallafa, ya bayyana cewa, ana ta kara wallafa rahotannin kin jikin Amurka da na kasashen yamma a kafofin sada zumunta, tare da sukar gwamnatin Biden da Harris, kan yadda suka boye tarin alluran riga kafin ba tare da an fitar da su don a yiwa jama’a ba.

Haka kuma, Amurka ta toshe kunnenta kan yadda cutar ke kara tsananta a kasashe kamar Indiya da Brazil, wadanda ke zama na daya da na biyu bi da bi da cutar ta fi kamari a duniya.

Cibiyar nan ta Duke ta kasa da kasa mai kula da harkar kiwon lafiya, ta ce jaridar TOI ta yi nuni da cewa, Amurka za ta kara samun alluran riga kafin fiye da kima har sama da miliyan 300 ko wasu karin riga kafin nan da watan Yuli, yayin da kasashe da dama sai sun jira shekaru, kafin su kammala yin riga kafin a kasashensu. Bari kashi a ciki dai ba ya maganin Yunwa. (Ibrahim Yaya)