logo

HAUSA

Kasar Sin jigon ci gaban tattalin arzikin duniya

2021-04-21 19:37:49 cri

Kasar Sin jigon ci gaban tattalin arzikin duniya_fororder_2N72SR

A wannan mako ne aka bude taron shekara-shekara na dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin Asiya na Boao na bana, taron dake zama karo na 20, tun bayan kafa wannan dandali a shekarar 2001. Haka kuma, shekaru ashirin cif ke nan da kasar Sin ta shiga kungiyar cinikayya ta duniya (WTO).

Daga shekaru ashirin din da suka gabata zuwa yanzu, kasar Sin na zama kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, duk da annobar COVID-19 dake ci gaba da addabar wasu sassan duniya.

Asusun ba da lamuni na duniya (IMF) ya bayyana cikin hasashensa na shekarar 2020 da 2021 cewa, kasar Sin ta ba da gudummawar kaso 60 cikin 100 na ci gaban tattalin arzikin duniya. Kana a shekarar 2025, Sin za ta ba da karin sama da kaso 30 cikin 100 na ci gaban tattalin arzikin duniya, idan aka kwatanta da kaso 10 cikin 100 da Amurka za ta bayar ga bunkasar tattalin arzikin duniya. Shin mene ne sirrin ci gaban kasar Sin da ma irin gudummawar da take bayarwa ga ci gaban tattalin arzikin duniya?

Masana na cewa, na farko tsarin raya tattalin arziki da zuba jari da mahukuntan kasar Sin suka fito da su, sun dace da halin da ake ciki, da ma tsarin kasar baki daya, baya ga kasancewarta babbar kasuwa mai cike da damammanki. Haka kuma Sinawa mutane ne masu basira da aiki tukuru, matakin da shi ma ya taka muhimmiyar rawa ga ci gaban kasar da ma duniya baki daya. Na biyu, Saurin farfadowar ayyukan masana’antu a kasar daga annobar COVID-19, matakin dake zama injin din bunkasa tattalin arzikin duniya a halin yanzu, kuma dandalin Boao na da muhimmanci a wannan fanni. A hannu guda kuma, kasashen Sin da Amurka dake zama manyan kasashe mafiya karfin tattalin arziki a duniya, sun bayyana kudirinsu na magance matsalar sauyin yanayi, ta hanyar rage fitar da iskar dake gurbata muhalli.

A jawabin da ya gabatar a yayin bikin bude taron dandalin Boao na bana, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, kasar Sin ta cimma nasarori da samun ci gaba, tare da sauran sassan Asiya da ma duniya baki daya. A halin da ake ciki yanzu, adalci shi ne abin da duniya take bukata ba danniya ba, da tafiyar da al’amuran duniya ta hanyar tuntuba da tattaunawa mai zurfi, kana daukacin kasashen duniya su shiga a dama da su wajen kyautata makomar duniya.

Wajibi ne a nuna adawa da matakin duk wata kasa ko wasu tsiraru na kakaba akidu ko ka’idojinsu kan sauran kasashe, ko kuma ba da dama ga wani ra’ayi da wata kasa ita kadai ta dauka wajen zama wata ka’ida ga daukacin duniya. Domin mai daki shi ya san inda yake masa Yoyo.

Sanin kowa ne cewa, tasirin sauye sauye, da annoba dake addabar wannan karni, sun haifarwa duniya wani irin yanayi na rashin tabbas, da kuma sauyin al’amura, baya ga rashin daidaito dake karuwa, yayin da duniyar yau ke fama da kalubale da damammaki daban daban. Wannan ya sa shugaban na Sin ya ba da shawarar sanya daidaito, da martaba juna da aminci tsakanin sassan kasashen duniya gaban komai, yayin raya alakar su. Hannu daya, ba ya daukar jinka

Kasar Sin ta sha nanata cewa, ba za ta taba neman yin babakere, ko fadada ikon ta, ko yin tasiri na danniya ba, duk kuwa da irin karfi da ci gaban da za ta iya samu. Kaza lika Sin ba za ta shiga duk wata takara ta makamai da kasashen duniya ba. Amma, za ta kare ’yanci da muradu da tsaro da ma moriyarta a duk lokacin da bukatar hakan ta taso ba.

Wani muhimmin batu shi ne, yayin da ake raya tattalin arziki a duniya bisa tsarin bai daya, ba a hana bude kofa ga kasashen waje da yin hadin gwiwa da juna, sannan duk wani kokari na kawo cikas da kare kai, da ficewa daga tsarin huldar kasa da kasa, sun saba ka’idojin tattalin arziki da kasuwanci na duniya, kuma wanda ya yi hakan, shi ne zai dandana kudarsa. Tsuntsun da ya janyo ruwa, shi ruwa zai doka. (Ibrahim Yaya)