logo

HAUSA

Yaushe za’a yi wa al’ummomi marasa rinjaye adalci a Amurka?

2021-04-21 22:21:33 CRI

Yaushe za’a yi wa al’ummomi marasa rinjaye adalci a Amurka?_fororder_1

Bayan da aka shafe tsawon makonni uku ana sauraren karar da aka shigar kan dan sanda farar fata Derek Chauvin bisa tuhumarsa da laifin kashe matashi dan asalin Afirka George Floyd a wata kotu dake jihar Minnesota ta kasar Amurka, a karshe ta yanke hukunci, inda aka tabbatar da cewa dan sandan ya aikata wasu laifuffuka uku.

A jawabin da ya gabatar bayan yanke wannan hukunci, shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana cewa, hukuncin da aka yanke, wani babban ci gaba ne da Amurka ta samu a fannin yaki da nuna wariyar launin fata. Amma duk da haka, jama’a da yawa suna ganin cewa, wannan hukunci ya sa dan sanda Chauvin ya dauki alhakin mummunan abun da ya aikata kawai, wato bai yiwa marigayi Floyd adalci ba. Wani dan siyasar Amurka mai suna Bernie Sanders ya ce, ba za’a samu ainihin adalci a Amurka ba, muddin ba a kawar da matsalar nuna wariyar launin fata da sauran wasu ayyukan keta hakkin dan Adam tun daga tushe ba, ciki har da gudanar da ayyuka ta hanyar da ba ta dace ba da ‘yan sandan kasar suka yi.

Yaushe za’a yi wa al’ummomi marasa rinjaye adalci a Amurka?_fororder_2

Duba da yadda aka shafe daruruwan shekaru ana gudanar da tsarin danniya, matsalar nuna wariyar launin fata ta zama ruwan dare a Amurka, wato hukunci daya kacal, ba zai kai ga warware matsalar ba. Rahotanni daga jaridar New York Times sun ce, a cikin makonni ukun da aka shafe ana sauraron karar Chauvin, ‘yan sanda suna kashe mutane akalla uku a kowace rana a Amurka, kuma fiye da rabinsu ‘yan asalin Afirka ne ko ‘yan asalin Latin. Abun takaici a nan shi ne, sa’o’i kalilan bayan da kotun ta yankewa Chauvin hukuncin, ‘yan sanda sun bindige wata ‘yar asalin Afirka mai shekaru 15 kawai a jihar Ohio.

Wannan na nufin cewa, wani abun bakin-ciki na nuna kabilanci wanda ya jawo adawa daga duk duniya, bai yi tasiri ko kadan kan ‘yan sandan Amurka ba, wato ba su gyara halayensu ko kadan ba.(Murtala Zhang)