logo

HAUSA

Ya kamata kasar Amurka ta koyi fasahar yin takara bisa wani nagartaccen yanayi

2021-04-19 16:37:20 CRI

Ya kamata kasar Amurka ta koyi fasahar yin takara bisa wani nagartaccen yanayi_fororder_0419-sharhi-Bello

Kwanakin nan, Le Yucheng, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin, ya yi hira da wakilin kamfanin dillancin labaru na AP na kasar Amurka, inda Mista Le ya ce, kamata ya yi a gudanar da takara tsakanin kasar Sin da kasar Amurka bisa wani nagartaccen yanayi, maimakon karkashin wani yanayi na kiyayya da fada da juna. Maganar Le ta nuna bambancin dake tsakanin kasashen Sin da Amurka, ta fuskar ra’ayoyinsu kan huldar dake tsakaninsu, inda kasar Sin ke rika neman kafa wata kyakkyawar huldar takara bisa tushen daidaiwa daida, da ka’idojin kasa da kasa, yayin da kasar Amurka a nata bangare, ke rungumar tunanin yakin cacar baki, da na wani bangare daya ya samu riba, ta yadda wani bangare na daban tilas ya yi hassara.

Hakika a cikin jawabin farko dangane da harkokin waje da Joe Biden ya gabatar, bayan da ya zama shugaban kasar Amurka, ya ce kasar Sin ita ce “’yar takara mafi hadari” a idon kasar Amurka. Dalilin da ya sa kasar Amurka ke damuwa kan kasar Sin, shi ne domin ta ga yanayin tasowar kasar. A shekarar 2020, jimillar GDPn kasar Sin ta kai kashi 70% na GDPn kasar Amurka, yayin da yawan tattalin arizkin kasar Sin ya kasance kimanin 10% na adadin tattalin arzikin kasar Amurka wasu shekaru 20 da suka wuce. Wannan yanayi ya sa kasar Amurka tsayawa kan bakanta, musamman ta la’akari da wani tunanin da Turawa suke kira “the Thucydides Trap”, inda aka ce wata sabuwar babbar kasar da bata dade da tashi ba, tabbas za ta kalubalanci tsohuwar babbar kasa.

Sai dai salon tasowar kasar Sin ba wani nau’in tasowa da kasar Amurka da sauran kasashe yammacin duniya suka saba da ganinsa bane, inda kasar Sin ke tasowa ta hanyar zaman lafiya da lumana. Idan mun nazarci dabarun tasowar manyan kasashe masu ci gaban tattalin arziki dake yammacin duniya, za mu fahimta cewa, dukkan wadannan kasashe sun taba mulkin mallaka a wasu sassan duniya, gami da kwatan albarkatun kasa, a tarihinsu. Daga baya suka yi amfani da fifikonsu a fannonin kimiyya da fasaha, da aikin soja don neman yin mulkin danniya a duniya. Amma a nata bangare, kasar Sin ta samu matsayinta na wata babbar kasa mai tasiri a duniya ne, ta hanyar kokarin raya tattalin arzikinta, da aiwatar da ciniki da hadin gwiwa, karkashin yanayin samun dunkulewar kasashen duniya waje guda. Yayin da take kula da harkokin kasa da kasa, kasar Sin ta kan jaddada muhimmancin kasancewar bangarori masu fada-a-ji daban daban a duniya, da neman kafa wata al’umma mai kyakkyawar makomar bai daya ta daukacin dan Adam. Wannan manufa ba wani abun da kasar Amurka za ta iya fahimta ba ne, ganin yadda kasar Amurka ke kokarin janye jikinta daga hadin gwiwar kasa da kasa, da nacewa ga mai da moriyarta gaban komai.

Wani dalili na daban da ya sa kasar Amurka ke son yin fito-na-fito da kasar Sin, shi ne domin al’adar kasar ta nuna fin karfi a duniya. A fannin siyasa, kasar Amurka ta zama babbar kasar dake jagorantar kasashen yammacin duniya bayan babban yakin duniya na biyu, kana ta lashe hadaddiyar kasashen Sobiet ta yakin cacar baki na shekaru 44. A fannin tattalin arziki, kasar Amurka ta tabbatar da wani tsari na yin amfani da kudin dalar Amurka wajen gudanar da cinikayyar kasa da kasa a duniya, kana kullum tana daukar matakai na hada-hadar kudi, wajen takara da sauran kasashe, gami da kwatan dukiyoyinsu. Sa’an nan a fannin aikin soja, kasar ta gudanar da yake-yake a kasashen Panama, da Iraki, da Afghanistan, da Somalia, da Sebia, da kuma Haiti, cikin shekaru fiye da 30 da suka wuce. Ta hanyar kwatan moriya daga sauran kasashe, kasar Amurka ta karfafa mulkinta na danniya a duniya.

Saboda haka, lokacin da kasar Amurka ta ga alamar tasowar kasar Sin, kawai sai ta tuna da matakan matsawa kasar Sin lamba, da fito-na-fito da ita. Amma wasu abubuwan da ba ta fahimta su ne:

Na farko, ana samun sauyawar yanayi a duniyarmu. A shekarar 2000, a wasu kasashe 8 masu sukuni, wadanda suka fi karfin tattalin arziki a duniya, GDPn su ya kai kashi 47% na daukacin tattalin arzikin duniya. Sai dai wannan adadi ya sauka zuwa kashi 34.7% zuwa shekarar 2018. Dalilin da ya sa haka, shi ne tasowar kasashe masu sabbin kasuwanni irinsu Sin, da Indiya, da Brazil da dai sauransu, lamarin da ya canza yanayin tattalin arzikin duniya. Bisa hasashen da cibiyar nazarin ayyukan ci gaban kasa ta majalisar gudanarwar kasar Sin ta yi, yawan tattalin arzikin kasashe masu tasowa zai kai kashi 60% na daukacin tattalin arzikin duniya, zuwa shekarar 2035. Ta la’akari da wannan yanayi na samun sauyi a duniya, kasar Amurka ba za ta samu damar kare matsayinta na fin karfi ba.

Na biyu shi ne, yadda ake dambarwa da kasar Sin ba zai daidaita rikice-rikicen dake cikin gidan kasar Amurka ba. Tun daga shekarun 1980, kasar Amurka ta fi dogaro kan hada-hadar kudi, da bangaren fasahohin zamani, wajen raya tattalin arzikinta. Sai dai wadannan bangarori guda 2 ba su cika samar da guraben aikin yi ba. Lamarin da ya haddasa lalacewar masana’antun hada kayayyaki a kasar, da karuwar mutane marasa ayyukan yi, da masu kankantar kudin shiga. Kana kudin kasar ya fi zama a hannun mutane kalilan. Wannan shi ne babban dalilin da ya sa ake samun wasu rikice-rikice a kasar Amurka. Don daidaita wannan matsala, ya kamata kasar Amurka ta aiwatar da cikakkiyar kwaskwarima kan tsarin tattalin arzikinta, maimakon daukar matakan matsawa sauran kasashe lamba, da ta da rikici da hargitsi a duniya.

Kana abu na uku shi ne, kasar Sin ba za ta taba baiwa kasar Amurka damar cin zarafinta ba. Yanzu haka jama’ar kasar Sin na kokarin gina tsarin gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin, karkashin jagorancin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, inda dukkan al’ummomin kasar ke mai da cikakken hankali kan ayyukan raya kasa, da al’ummomi, da neman tabbatar da jin dadin zaman rayuwarsu. Hadin kan jama’ar kasar da yawansu ya kai biliyan 1.4, da cikakken goyon bayan da suke bawa gwamnatinsu, sun sa kasar Sin na iya murkushe duk wani mummunan yunkuri na cin zarafinta.

Kamar yadda Le Yucheng, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin, ya fada, ya kamata a daidaita huldar dake tsakanin Sin da Amurka don samar da alfanu ga duniya. Yayin da kasar Amurka ke fuskantar aikin tinkarar annobar COVID-19, da na farfado da tattalin arziki, ya kamata ta karbi shawarar da kasar Sin ta ba ta, ta fara hakuri, da hadin gwiwa da sauran kasashe, gami da yin takara bisa wani nagartaccen yanayi, maimakon ci gaba da taho-mu-gama da kasar Sin, ta yadda za ta samar da gudunmowa ga tabbatar da zaman lafiya da ci gaban duniyar, wadda za ta dace da matsayinta na wata babbar kasa. (Bello Wang)

Bello