logo

HAUSA

Kasashen Afirka sama da 40 sun halarci shirin “Ziri daya da hanya daya”

2021-04-16 14:44:09 CRI

Kasashen Afirka sama da 40 sun halarci shirin “Ziri daya da hanya daya”_fororder_210416-bayani-Maryam-hoto

“Ajandar shekarar 2063” ta bayyana burin kasashen Afirka na raya nahiyar baki daya, da ma fatan al’umma wajen samun ci gaba. Kuma, shirin “Ziri daya da hanya daya” ya samar da damammaki ga gamayyar kasa da kasa wajen raya tattalin arziki da aiwatar da “Ajandar shekarar 2030 ta MDD”. A karshen shekarar 2020, kasar Sin da kungiyar tarayyar kasashen Afirka wato AU suka kulla “shirin hadin gwiwar Sin da AU game da inganta ‘shirin ziri daya da hanya daya’”, domin hada shirin “Ziri daya da hanya daya” da “Ajandar shekarar 2063” ta kungiyar AU tare, ta yadda za a tabbatar da samun bunkasuwa mai inganci a kasashen Sin da Afirka.

Ga Karin bayani daga Maryam Yang…

A ranar 7 ga watan Janairu, yayin da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi yake ziyara a kasar Botswana, bangarorin biyu sun kulla wasu yarjejeniyoyi game da karfafa hadin gwiwar kasashen biyu wajen inganta shirin “Ziri daya da hanya daya”, matakin da ya sa, kasar Botswana ta zama kasa ta 46 da ta shiga shirin “Ziri daya da hanya daya”.

Nahiyar Afirka muhimmiyar nahiya ce cikin shirin “Ziri daya da hanya daya”, a halin yanzu, kasashen Afirka sama da 40 da kwamitin kungiyar AU sun riga sun kulla yarjejeniyar hadin gwiwa karkashin shirin “Ziri daya da hanya daya”, adadin da ya kai kashi 1 bisa 3, bisa yawan kasashe da kungiyoyin kasa da kasa wadanda suka kulla wannan yarjejeniya.

Kuma, shirye-shiryen gina layukan dogo, da tituna, da filayen jiragen sama, da tasoshin jiragen ruwa, da kuma tasoshin samar da wutar lantarki da sauransu, sun taka muhimmiyar rawa wajen raya tattalin arziki da zaman takewar al’umma a nahiyar Afirka.

“Suna na Demi Jimoni, ina zama a garin Voi.”

Demi Jimoni wani fasinja ne dake bin jirgin kasan dake tsakanin Mombasa da Nairobi wato SGR, yanzu, yana aiki a wani garin dake da nisan kilomita 300 daga birnin Nairobi na kasar Kenya, kuma, yana komawa gida domin haduwa da iyalinsa a ko wane karshen mako sabo da saurin zirga-zirga na layin dogon SGR. Ya ce, wannan layin dogo ya canja zaman rayuwar al’umma.

“Bin layin dogon dake tsakanin Mombasa da Nairobi, shi ne hanya mafi kyau ta yin tafiye-tafiye mai nisa, domin yana da sauri, da tsaro da kuma dadin zama, har ma, ana da wurin sayar da abinci da sauransu cikin jiragen kasa dake tafiya kan layin.”

Cikin shekaru 11 da suka gabata, kasar Sin ta kasance kasar da ta fi musayar ciniki da kasashen Afirka, kuma, ta kasance babbar kasa dake zuba jari a nahiyar Afirka, lamarin da ya sa, ta ba da gudummawar karuwar tattalin arziki da sama da 20% a duk fadin nahiyar Afirka cikin shekaru da dama da suka gabata.

“5 4 3 2 1”

“An sayar duka!”

A tsakiyar watan Mayu na shekarar 2020, wasu manonan waken kofi suna kallon wani shirin kasuwanci ta yanar gizo, inda aka sayar da waken kofi kai tsaye. Bayan sayar da dukkanin waken kofin, sun yi murna kwarai da gaske. Mataimakiyar babban magatakardan MDD, kana, babbar sakatariyar hukumar kula da tattalin arzikin Afirka ta MDD Vera Songwe ta bayyana cewa, za a samar da karin amfanin gona na Afirka zuwa kasar Sin ta shirin kasuwanci ta yanar gizo na kasar Sin, bisa karuwar musayar hajoji a tsakanin bangarorin biyu, ta yadda, za a taimakawa manoman nahiyar Afirka kawar da talauci.

Shugaban tawagar jakadun nahiyar Afirka dake kasar Sin, kana, jakadan kasar Kamaru dake kasar Sin Martin Mpana ya bayyana cewa, shirin “Ziri daya da hanya daya” ya samar da damammaki ga kasashen Afirka wajen neman bunkasuwa, yana fatan samun Karin kasashen Afirka da za su shiga wannan shiri, ya ce,“Shirin “Ziri daya da hanya daya” wani shiri ne dake son hada kan bangarori daban daban, a maimakon, hadin gwiwar wasu kamfanoni ko kungiyoyi, duk wanda yake da sha’awa, zai iya shiga wannan shiri. Shi ya sa, muke samun karin kasashen dake shiga wannan shiri, domin zai samar mana karin damammakin samun ci gaba. A nan gaba, za mu ci gaba da inganta wannan shiri domin shimfida zaman lafiya da wadata cikin kasa da kasa.” (Mai Fassarawa: Maryam Yang)