logo

HAUSA

Amurka Ba Za Ta Cimma Nasarar Dakile Kasar Sin Ta Fakewa Da Batun Audugar Yankin Xinjiang Ba

2021-04-14 15:03:26 CRI

Amurka Ba Za Ta Cimma Nasarar Dakile Kasar Sin Ta Fakewa Da Batun Audugar Yankin Xinjiang Ba_fororder_src=http___img1.cache.netease.com_catchpic_E_E0_E0D11409B84E64645BA2CDFFE7E5DDA1&refer=http___img1.cache.netease

Shekarun baya-bayan nan, Amurka ta rika fakewa da batun “hakkin Bil Adama” don kakabawa sana’ar audugar yankin Xinjiang takunkumi, tana mai cewa wai ana tilasawa mutane kwadago a wannan fanni. To ko me ya sa Amurka ta zabi sana’ar auduga?

Da farko, sana’ar auduga ginshigi ne a sana’ar noma a yankin. Alkaluma da hukumar kididdigar ta kasar Sin, da ta yankin Xinjiang suka fitar, sun bayyana cewa, ya zuwa shekarar 2020, yawan audugar da yankin ya samar, ta haura ton miliyan 5.16, wanda ya kai kashi 87% na dukkan wadda ake samarwa a duk fadin kasar Sin. Ya zuwa karshen shekarar 2019, yawan kamfanoni dake aikin yadi da tufafi a yankin ya kai 3251.

Alkaluman dake nuna cewa, wannan sana’a ta ba da gudunmawa matuka ga bunkasuwar tattalin arzikin yankin Xinjiang.

Sannan an ce, manoman da suka kai kaso 50% bisa na dukkan manoman yankin, suna noman auduga a yankin, kuma manoma na kananan kabilu sun kai sama da kaso 70%. A hannu guda kuma, yawan guraben aikin yi da aka samar a wannan fanni a shekarar 2019 ya kai dubu 135, hakan ya sa wannan sana’a ya zama muhimmiyar hanyar kawar da fatara a yankin.

Ban da wannan kuma, sana’o’i dake da alaka da wannan fanni na kunshe da shuka, da girba, da kuma sayarwa, da sarrafa auduga da sauransu. Don haka in an kakabawa takunkumi kan duk wani bangare cikin wadannan sana’o’i, hakan zai haifar da bala’i ga dimbin ma’aikata da iyalansu.

Amurka na fakewa da batun “tilasta kwadago”, don kakabawa wasu kamfanonin yankin takunkumi, wanda hakan zai jefa manoma da ma’aikata masu dimbin yawa wadanda ke aiki cikin wannan sana’a a mawuyancin hali na rashin aikin yi. Wasu kuma da suka fita daga kangin talauci a ’yan shekarun baya, za su sake komawa halin fama da talauci, har ta kai sun fuskanci kalubale na rayuwa.

A cikin shekaru 20 da suka gabata, an samu dubban ayyukan ta’addanci a yankin Xinjiang, wadanda suka haifar da barazana ga rayuka da dukiyoyin fararen hula. A gaban wadannan ayyukan ta’addanci da mazauna yankin Xinjiang suka yi fama da su, Amurka ta yi kunnen uwar shegu da hakan. Amma, da ganin ba a samu ayyukan ta’addanci a yankin har tsawon kusan shekaru 5 a jere ba, kuma jama’a na zaman rayuwa cikin nishadi, sai ta fara jin tsoro, ta fito ta fara tayar da hankula a yankin.

A shekarun baya-bayan nan, Amurka ta rika zargin manufofin da gwamnatin Sin ke aiwatarwa bisa sunan wai kare “hakkin bil Adama”, ta saka takunkumi kan ’yan sanda na yanki wadanda suke yakar ta’addanci. Daga bisani ta kakabawa ma’aikatan kawar da tsattsauran ra’ayi takunkumi. Yanzu haka kuma tana kakabawa sana’ar auduga takunkumi, wadda jama’ar yankin ke dogaro da ita. Shin ko “hakkin bil Adama” a bakin Amurka na nufin sanyaya gwiwar sana’ar da yankin ke matukar dogaro da ita, da murkushe tattalin arzikinsa, matakin da zai haifar da rashin aikin yi, har wadannan ’yan kabilar Uygur su sake fadawa cikin ta’addanci da tsattsauran ra’ayi? Amma, auduga ba za ta zama makamin Amurka na dakile ci gaban kasar Sin ba ko kadan.

Amma don me Amurka take matukar son shiga tsakanin harkokin kasar Sin, dalili shi ne, bunkasuwar kasar Sin da kwanciyar hankali da zaman lafiya mai dorewa a yankin Xinjiang, sun saba da tunanin Amurka na amfani da ta’addanci don dakile kasar Sin, wanda ya zama mummunan matakin da Amurka ta kan aiwatar, don kawo baraka a sauran kasashe.

A hakika dai, Amurka ba ta kula da batun hakkin bil Adama ko kadan ba, kuma abun da take kulawa shi ne shafawa manufofin da gwamnatin Sin ke dauka kan yankin Xinjiang, bisa sunan kare hakkin “bil Adama”, ta yadda za ta hana bunkasuwar kasar Sin. Amma fa, Sin ba kasar Iraqi ko Libya balle Sham ba ce, ba ta jin tsaron Amurka ko kadan ba, makarkashiyar Amurka ba za ta cimma nasara ba. (Amina Xu)