logo

HAUSA

Mazaunen kauyen Guza Kanti Kanti na jihar Xinjiang suna jin dadin zaman rayuwa

2021-04-14 11:31:04 CRI

Kauyen Guza Kanti, wani kauye ne dake yankin Kashgar na jihar Xinjiang ta kasar Sin. An shuka borkono a tsakanin itatuwan Badam. Yayin da ‘yan jarida suka ziyarci kauyen a kwanakin baya, sun ga mazaunen kauyen suna sauyawa borkonon matsuguni. Wannan na nuna cewa, za a girbe borkonon ne a lokacin kaka, matakin da zai inganta rayuwarsu.

“A baya ina shuka auduga a gonar da ta kai fadin murabba’in mita fiye da dubu 6, da kuma borkono a gonar da ta kai murabba’in mita fiye da dubu 3. Yawan kudin shiga da na samu daga noman auduga a kowane fadin murabba’in mita 667 ya kai Yuan dubu 1, yayin da yawan kudin da nake samu daga noman borkono ya kai Yuan dubu 4, wanda ya ninka na auduga har sau 4. Don me ba za mu rika shuka borkono ba kawai?”

Wannan fasaha ce da Tohtigul Yusup ta yi amfani da ita wajen samun kudin shiga. Tana da gona da ta kai murabba’in mita kimanin dubu 10, a shekarar bara, ta yi amfani da gona mai murabba’in mita fiye da dubu 3 wajen shuka borkono, inda ta samu Yuan dubu 20 a shakara a matsayin kudin shiga. Domin kara samun kudin shiga daga borkono, a bana ta ninka yawan borkono da take shukawa har sau biyu.

Akwai iyalai 384 da ya kunshi mutane 1734 a kauyen Guza Kanti, a lokacin da iyalai 181 da ya kunshi mutane 842 suka yi rajista a matsayin masu fama da talauci. Don taimakawa yaki da talauci a kauyen, kwamitin harkokin kauyen ya kafa kungiyar hadin gwiwar aikin gona, inda aka maida shuka kayan lambu na musamman kamar borkono a matsayin wata dabarar samun kudin shiga ta hanyar biyan bukatun kasuwa. Kungiyar ta samar da fasahohi ga mazaunen kauyen, da ma saukaka fannonin shuka, da yin amfani da taki, da ban ruwa, da sayar da amfanin gona da sauransu don warware matsalolinsu. Tohtigul Yusup ta bayyana cewa, “Da farko kwamitin harkokin kauyen, ya samar mana da fasahohin shuka da taki kyauta, da kuma warware matsalolinmu na yin amfani da ruwa yayin da muke shuka borkono.”

Jami’in rukunin aiki dake kauyen Guza Kanti Li Jun ya yi bayanin cewa, rukuninsa ya dauki matakan bada taimako bisa yanayin kowane iyali, ban da yaki da talauci, sun kuma koyar musu fasahohi da za su yi yaki da talauci da kansu. Ya ce, “Bayan da aka gudanar da ayyukan yaki da talauci a kauyen, mazaunen kauyen sun koyi sabbin tunani da hanyoyin yaki da talauci, kana sun koyi dabarun neman kudin shiga da kansu.”

Akwai mutane 5 a iyalin Tubuhan Ruzi, babbar ‘yarsa ta yi karatu a makarantar midil dake birnin Urumqi, dansa da karamar ‘yarsa sun yi karatu a makarantar firamare dake kauyen. Game da zaman rayuwarsa, Tubuhan Ruzi ya ce ya gamsu sosai. Ya ce, “Na gamsu sosai da yadda nake aiki da zaman rayuwa, ina godiya ga jam’iyyar kwaminis ta Sin da shugaban kasar Sin Xi Jinping da kuma jami’an gwamnatin kauyenmu.”

A watan Nuwanba na shekarar 2020, an cimma burin kawar da talauci a dukkan kauyen Guza Kanti, yawan kudin shiga da kowane mutum a kauyen yake samu a kowace shekara ya kai Yuan dubu 11. A matsayinsa na jami’in rukunin aiki dake kauyen, Li Jun yana alfahari, yana cewa, yanzu mazauna kauyen sun fita daga talauci, bayan da aka tabbatar da zaman rayuwarsu, a nan gaba kuma, jami’an gwamnatin kauyen za su yi tunanin yadda za a kyautata zaman rayuwar mazauna kauyen da al’adun kauyen.

A sabon filin nuna al’adu na kauyen da aka kafa, Li Jun ya yi bayani game da kyakkyawar makomar kauyen Guza Kanti. Ya ce, jami’an kauyen suna shirin gina masaukan baki na musamman da tsara ayyuka masu ban sha’awa a kauyen, kuma nan ba da jimawa ba, masu yawon shakatawa daga wurare daban daban za su fara kawo ziyara kauyen. A don haka, ana maraba da duk wanda dake da niyyar kawo ziyara kauyen Guza Kanti don jin dadi a wurin. (Zainab)