logo

HAUSA

Farfadowar Wuhan Ya Nuna Yadda Kasar Sin Ta Sauke Nauyin dake Bisa Wuyanta

2021-04-08 20:59:03 CRI

Yanzu haka a birnin Wuhan na kasar Sin, an shiga lokacin bazara mai dumi, inda masu yawon shakatawa da dama suke ji dadin kallon furanni, baya ga cunkuson mutane a titunan kasuwancin birnin, sa’an nan, da dare ana iya ganin yadda aka kawata alamar birnin wato hasumiyar Huanghelou da fitilu da dare. A ranar 8 ga watan Afrilun bara, an maido da zirga-zirga a tsakanin birnin Wuhan da sauran sassan kasar Sin, wanda aka dakatar da zirga-zirga na kwanaki 76 a tsakaninsa da sauran wuraren kasar. Abun da ya kamata a lura da shi ne duk da barkewar annobar COVID-19, Wuhan ya kasance daya daga cikin birane guda 10 mafi karfin tattalin arziki a kasar Sin a shekarar 2020.

Birnin Wuhan ya farfado ne cikin shekara guda kawai, lamarin da ya sake nuna cewa, matakin da kasar Sin ta dauka na dakatar da zirga-zirga a tsakanin Wuhan da sauran sassan kasar ya yi daidai, wanda kuma yake da matukar muhimmanci wajen dakile yaduwar annobar. Har illa yau kasashen duniya sun gane wa idanunsu cewa, kasar Sin ta yi yaki da annobar tare da komawa bakin aiki da dawo da harkokin kasuwanci da na samar da kayayyaki yadda ya kamata, haka kuma ta yi iyakacin kokarinta wajen yaki da annobar a duniya da kuma farfado da tattalin arzikin duniya. Ta kuma samar wa kasashen duniya abun rufe baki da hanci fiye da biliyan 220, bai wa kasashe fiye da 150 da kungiyoyin kasa da kasa 10 tallafawa, har ma ta ba da tallafin alluran rigakafin COVID-19 ga kasashe fiye da 80 da kungiyoyin kasa da kasa 3. Kasashen duniya suna ganin cewa, kasar Sin ta ba da nata gudummowa wajen yin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa kan yaki da annobar, wadda babu kamanta.

A sa’i daya kuma, farfadowar tattalin arzikin kasar Sin ba tare da wata matsala ba, ta kara azama ga farfadowar tattalin arzikin duniya a shekara guda da ta gabata, wanda ya samu koma baya. A shekarar 2020, jimillar tattalin arzikin kasar Sin ta wuce kudin Sin RMB yuan triliyan 100, ta zama kasa daya kacal a duniya wadda ta samu karuwar tattalin arziki, lamarin da ya taimaka sosai wajen tabbatar da kwanciyar hankali a masana’antun duniya. A kwanan baya, asusun ba da lamunin duniya wato IMF ya kaddamar da rahotonsa na hasashe kan tattalin arzikin duniya, inda ya yi hasashen cewa, yawan karuwar tattalin arzikin duniya zai kai 6% a shekarar 2021, kuma tattalin arzikin kasar Sin zai karu da 8.4%, adadin da ya wuce hasashen da ya yi a baya. Kasar Sin wadda ke gaggauta kafa sabon fasalin raya kasa, za ta kara bai wa duniya damar samun nasara tare.

Ya zuwa yanzu, wasu ‘yan siyasan kasashen yammacin duniya sun sanya siyasa kan aikin binciken gano asalin annobar a duniya da batun rigakafi, a yunkurin ci gaba da bata sunan kasar Sin. Amma ci gaban Wuhan da kokarin kasar Sin wajen yaki da annobar a duniya sun karyata zarginsu kwata kwata. Kasar Sin wadda ke sauke nauyin dake bisa wuyanta, za ta kara kuzari kan yaki da annobar a duniya da kuma farfado da tattalin arzikin duniya. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan