logo

HAUSA

Yaki Da Talauci Bisa Yanayin Da Ake Ciki, Sabuwar Hanya Ce Ta Rage Talauci

2021-04-07 21:07:04 CRI

Kwanan baya, kasar Sin ta fitar da takardar bayani mai taken "Rage talauci: kwarewar kasar Sin da gudummawarta”, inda ta fayyace cewa, ya zuwa karshen shekarar 2020, kasar Sin ta cika alkawarinta na yaki da fatara, ta fitar da dukkan mazauna yankunan karkara miliyan 98.99 daga kangin talauci, adadin da ya wuce kaso 70 cikin 100 na jimillar wadanda aka fitar da su daga kangin talauci a duniya bisa ma’aunin bankin duniya. Haka kuma kasar Sin ta cimma nasarar manufofin kawar da talauci kamar yadda yake kunshe cikin ajandar samun ci gaba mai dorewa na MDD nan da shekarar 2030, shekaru 10 kafin lokacin da aka tsara.

Ta yaya kasar Sin ta cika alkawarin da ta yi? Ta yaki da fatara daidai bisa yanayin da ake ciki a kasar. Matakin yaki da talauci daidai bisa yanayin da ake ciki, sirrin kasar Sin ne mai muhimmanci wajen samun nasarar fitar da dukkan al’ummarta daga talauci, haka kuma wata sabuwar hanya ce da ‘yan Adam ke bi wajen rage talauci. A nahiyar Afirka, kasar Sin tana gudanar da ayyukan yin hadin gwiwar fasaha a tsakaninta da kasashen Afirka ta fuskar raya ababen more rayuwar jama’a, aikin gona, kiwon lafiya da dai sauransu.

Yadda kasar Sin ta fitar da dukkan al’ummarta daga kangin talauci bisa lokacin da aka tsara, ya sanya sauran kasashen duniya gane cewa, muddin aka nuna jarumtaka, da hangen nesa, da sauke nauyi bisa wuya, da bin hanyar da ta dace wajen rage talauci, to, ‘yan Adam za su samu ci gaba har ma su fitar da kansu daga fatara da kuma samun ci gaba tare. Don haka ma iya cewa, nasarorin da kasar Sin ta samu wajen rage talauci da kuma kyawawan fasahohinta, ba ita kadai ta amfana ba, har ma ta amfani duniya baki daya. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan