logo

HAUSA

Ya Zama Tilas Jaridar LeMonde Ta Nemi Gafara Daga Sassa Masu Ruwa Da Tsaki

2021-04-04 20:55:31 CRI

Kwanan baya, shahararriyar jaridar LeMonde ta kasar Faransa ta yi wa CGTN na kasar Sin suka cewa, wata ‘yar jaridar CGTN wai ita Laurène Beaumond ta rubuta wani bayani dangane da batutuwan ‘yan kabilar Uygur da Taiwan na kasar Sin a kafofin yada labaru mallakar gwamnatin kasar Sin. Ita Laurène Beaumond, a zarihi babu ita a duniya, amma tana kare sunan kasar Sin dangane da manufofin jihar Xinjiang.

A ganin jaridar LeMonde, wannan mace wai ita Laurène Beaumond ta bayyana ra’ayinta ne bisa umurnin gwamnatin kasar Sin, wato babu kisan kare kangi a jihar Xinjiang. Jaridar ta LeMonde ba ta maida hankali kan ko bayaninta ya dace da hakikanin abubuwa ko a’a, ta nuna shakka kan ko wannan ‘yar jarida tana kasancewa a duniya ko a’a. Ko akwai wata mace mai suna Laurène Beaumond ko a’a?

A shekarun baya, ‘yan jaridun Faransa ba sa maida hankali kan ko labarunsu sun dace da hakikanin gaskiya ko a’a. Abu daya kacal da suke maida hankali a kai shi ne ko ra’ayoyinsu sun yi daidai ta fuskar siyasa ko a’a. Dukkan abubuwan da suka ambato dangane da kasar Sin suna bata sunan kasar Sin, yayin da suka mayar da bayanan da suka kusan yin daidai da na ra’ayoyin kasar Sin, a matsayin karya ce da gwamnatin kasar Sin ta yi.

Duk da haka hakikanin abubuwa da kuma abubuwan da suka faru a tarihi sun sanya jaridar LeMonde ta yi amai kuma ta lashe. Kafofin yada labaru na Faransa sun sake yin bincike sun kuma gano cewa, Laurène Beaumond tana rayuwa a duniya, ta gama karatu daga jami’a a Faransa. Har ma jaridar Le Figaro ta Faransa ta zanta da Laurène Beaumond. Me ya sa babu sunanta cikin jerin sunayen ‘yan jarida da suka yi rajista a Faransa? Saboda ba ta yi amfani da sunanta na gaskiya ba, tana amfani da sunan lakabi. To, me ya sa ta yi amfani da sunan lakabi? Saboda ‘yan jaridun da suka bayyana abun gaskiya, musamman bayanansu sun sha bamban da na manyan kafofin yada labarun kasar, su kan fuskanci babban matsin lamba ta fuskar siyasa, tattalin arziki da dai sauransu. Hakika dai, yanzu Laurène Beaumond tana fuskantar babban matsin lamba, tana matukar fargaba, kuma kila ta rasa wasu ayyuka.

Don haka ya kamata jaridar LeMonde ta nemi gafara a hukumance daga masu karanta jaridar, madam Laurène Beaumond, CGTN na kasar Sin. Kana kuma, bayanan jaridar sun illanta zumuncin da ke tsakanin Faransa da Sin. Ko jaridar zata nemi gafara ko a’a zai nuna yadda ta daidaita batun labarun da ba na gaskiya ba. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan