logo

HAUSA

Wayon Amurka Ba Zai Hana Ci Gaban Yankin Hong Kong Ba

2021-04-03 15:08:33 CRI

Wayon Amurka Ba Zai Hana Ci Gaban Yankin Hong Kong Ba_fororder_1

A kwanan nan ne ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta gabatarwa majalisar dokokin kasar wani rahoto dangane da dokar manufofi kan Hong Kong, inda ta tsoma baki cikin harkokin yankin Hong Kong, da sake jaddada cewa ba za ta ci gaba da baiwa yankin wani gatanci ba. Hakan ya nuna cewa, sabuwar gwamnatin Amurka dake karkashin jagorancin Biden tana ci gaba da aikata kuskure kamar yadda gwamnatin Trump ta yi, da yin shisshigi cikin harkokin cikin gidan kasar Sin, abun da ya jawo babbar adawa da takaici daga Sin.

Rahoton, wanda ke cike da jita-jita da karairayi, ya nuna cewa akwai wasu Amurkawa wadanda ke yunkurin hana ci gaban kasar Sin bisa hujjar yankin Hong Kong. Amma babu tantama yunkurinsu zai bi ruwa. A tsakiyar shekarar da ta gabata ne, Amurka ta sanar da dakatar da baiwa yankin Hong Kong gatanci, amma ba’a ga wani tasiri ba, domin Hong Kong na ci gaba da bunkasa yadda ya kamata. Rahoton binciken da kungiyar ‘yan kasuwan Amurka dake Hong Kong ta bayar ya nuna cewa, idan aka kwatanta halin da ake ciki a Hong Kong a watan Janairun bana da na watan Augustar bara, ana iya gano cewa, ana kara samun kamfanoni a Hong Kong wadanda suka nuna yakini da tabbaci ga yanayin gudanar da kasuwanci a wurin. Har ma akwai kamfanonin kasar Amurka da dama wadanda suka bayyana cewa, nan da shekaru uku masu kamawa za su fadada zuba jari a Hong Kong.

Wayon Amurka Ba Zai Hana Ci Gaban Yankin Hong Kong Ba_fororder_2

Dalilin da ya sa Hong Kong ta samu nasarori kamar haka, shi ne domin jajircewar da mazauna yankin suka yi zuriya bayan zuriya, gami da cikakken goyon-bayan da babban yankin kasar Sin ke samar mata, amma ba tare da dogaro kan zakka ko tallafi daga wata kasar waje ba.

Muna kira ga bangaren Amurka, da ya dakatar da ci gaba da aiwatar da manufofi da ba su yi daidai ba kamar yadda tsohuwar gwammatin Trump ta yi, wato ta daina yin katsalandan cikin harkokin Hong Kong ba tare da bata lokaci ba. Duk wata barazana ko sanya takunkumin da duk wata kasa za ta yi, ba zai taba taka birki ga ci gaban yankin Hong Kong ba.(Mai Fassara: Murtala Zhang)