logo

HAUSA

Harin da sojojin Barkhane na Faransa ya haddasa mutuwar fararen hula 19 a Mali

2021-03-31 09:34:34 CRI

A jiya ne, tawagar MDD dake aikin wanzar da zaman lafiya a kasar Mali (MINUSMA), ta fitar da wani rahoton bincike, game da wani hari ta sama da aka kai ranar 3 ga watan Janairun wannan shekara a yankin, inda ta yi ittifakin cewa, harin da dakarun kasar Faransa dake yaki da ‘yan ta’adda da ake kira Barkhane da aka girke a yankin suka kai, ya rutsa ne da galibin fararen hula dake halartar wani bikin aure.

A cewar rahoton, tawagar MINUSMA ta kuma tabbatar cewa, bikin ya halkara sama da fararen hula 100 a wurin da aka kai harin, ciki har da wasu mutane biyar masu dauke da makamai, da ake zargin mambobin kungiyar nan ce ta Katiba Serma.

MINUSMA ta bayyana a cikin rahoton nata cewa, ta samu bayanai dake tabbatar da cewa, sojojin na Barkhane, sun kashe a kalla mutane 22 a wannan rana, a yankin Bounty dake tsakiyar kasar ta Mali.

Binciken tawagar ya kuma tabbatar da mutuwar fararen hula 19, sakamakon harin da sojojin na Barkhane suka kaddamar, harin da a cewar rundunar sojan kasar Faransa, ta nufi kungiyar ‘yan ta’adda ne masu dauke da makamai.(Ibrahim)