logo

HAUSA

Tarayyar Turai na son zubar da kimarta a idon duniya

2021-03-23 17:14:35 CRI

Tarayyar Turai na son zubar da kimarta a idon duniya_fororder_微信图片_20210323161610

Kasar Sin, ta sanar da kakabawa wasu mutane 10, da kamfanonin Turai 4 takunkumi a jiya Litinin, inda ta ce ta kakaba su ne saboda yadda suka yi matukar lahanta moriyarta, kana suka yada karairayi, da farfaganda maras tushe game da ita.

Da alama dai, Tarayyar Turai na son yada girmanta, da zama ’yar amshin shatan Amurka. Abun da kowa ya sani ne cewa, kullum, Amurka na kokarin lahanta moriya da illata ci gaban kasar Sin da kuma kokarin tsoma bakinta cikin harkokinta na cikin gida, wanda ba komai yake haifarwa ba illa kara tsamin dangantaka a tsakaninsu. Kana Amurkar, ta sha kokarin ingiza Tarayyar Turai ta mara mata baya a cikin yunkurin nata na matsawa kasar Sin.

Alamu sun nuna cewa, Tarayyar Turai ta fara bin sawun Amurka, inda take yunkurin lalata dangantakar dake tsakaninta da Sin. Domin a jiya Litinin, ta sanar da kakaba takunkumai kan wasu daidaikun Sinawa da kamfanin kasar, tana mai dogaro da abun da ta kira batun take hakkokin bil Adama da cin zarafin musulmin Uygur a jihar Xinjiang ta kasar Sin, kamar dai yadda Amurka ke ikirari.

Cikin shekaru sama da 40 da suka gabata, adadin ’yan kabilar Uygur da Amurka ke ikirarin ana musu kisan kare dangi, ya karu daga miliyan 5.55 zuwa sama da miliyan 12. Kana cikin shekaru sama da 60 da suka gabata, jimillar tattalin arzikin Xinjiang ya karu sama da sau 200. Sannan matsakaicin tsawon shekarun haihuwa na mutanen jihar ya karu daga shekaru 30 zuwa 72. Haka zalika, yankin ya yi adabo da talauci kamar sauran yankunan kasar Sin. Duk wadannan kadan ne daga cikin shaidun dake nuna cewa, Sin na iyakar kokarin ganin ta kyautata zamantakewa tare da raya yanayin jihar Xinjiang.

Lokaci ya wuce da za a rika yi wa wata kasa tilas ko cin zalinta, musamman babbar kasa kuma jajirtacciya mai samun ci gaba cikin sauri kamar kasar Sin. Dole ne kasar Sin ta kare cikakken ’yanci da ikonta. Ya kamata kasashen duniya su fahimci cewa, duk da bil adama na da makoma ta bai daya, yanayin al’adu da tsarukan tafiyar da harkoki sun bambanta, don haka, ya kamata a kyale kowacce kasa ta zabi dabaru da tsarukan da suka dace da ita.

Shaidu sun nuna cewa, irin manufofin kasar Sin su ne suka kai ta ga matsayin da take a yanzu. Wato dai, kwalliya tana biyan kudin sabulu, don haka, ya kamata kasashen yamma su mayar da hankali wajen shawo kan matsalolin dake gabansu, maimakon mayar da hankali kan batutuwan da ba su shafe su ba. kuma ya kamata Tarayyar Turai a matsayinta na babbar kungiya mai kima a duniya, ta rike darajarta, ta dubi alfanun dake tattare da hadin gwiwarta da Sin, ta daina tsoma baki cikin harkokin da ba su shafe ta ba. (Faeza Mustapha)