logo

HAUSA

Jam’iyyar Kwaminis Ta Kasar Sin Na Mai Da Hankali Sosai Wajen Neman Ingantaccen Ci Gaba

2021-03-22 19:30:30 CRI

Jam’iyyar Kwaminis Ta Kasar Sin Na Mai Da Hankali Sosai Wajen Neman Ingantaccen Ci Gaba_fororder_hoto

Masu hikimar magana na cewa, “labarin zuciya a tambayi fuska”. A wani kaulin kuma, “in gani a kasa wai ana biki a gidan su kare.” Yayin da a wannan shekarar ake cika shekaru 100 da kafuwar jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin wato JKS, hankalin kasashen duniya ya fi karkata ne game da irin manyan nasarorin da kasar ta samu ta fuskar bunkasuwar tattalin arziki na kyautatuwar zaman rayuwar al’ummar Sinawa bisa kaiwa wani matsayi na matsakaiciyar wadata. Ko da yake, akasarin wadannan nasarori sun samo asali ne bisa ga irin jajurcewar da magabatan shugabannin jamhuriyar jama’ar kasar Sin suka nuna tun daga lokacin kafuwar jam’iyyar JKS mai mulkin kasar Sin har zuwa wannan lokaci da muke ciki. Alal misali, shugaban dake jan ragamar kasar Sin a halin yanzu wato shugaba Xi Jinping, ya jaddada aniyar bayar da cikakken fifiko wajen kula da lafiyar jama’a gami da gina ingantaccen tsarin samar da ilmi mai inganci tun daga tushe domin biyan muradun al’ummar kasa. Koda a makon da ya gabata ma, sai da babban sakataren kwamitin tsakiyar jam’iyyar kwaminis ta kasar ta Sin, ya yi tsokaci a lokacin taron ganawa da manyan jami’an kula da sha’anin ilmi na kasa, da jami’an kiwon lafiyar kasar a wani taron hadin gwiwa da suka gudanar. Shugaba Xi ya bukaci a mayar da hankali wajen warware matsalolin manyan cutukan dake damun lafiyar al’ummar kasa. Ya bayyana cewa, kasar Sin ta cimma manyan nasarori mafiya wahala a cikin sama da shekara guda, sannan ya yabawa jami’an kiwon lafiyar kasar wadanda ya ce sun sadaukar da rayuwarsu domin yaki da annobar COVID-19 a lokaci mafi hadari. A game da ilmi kuwa, shugaba Xi ya ce tilas ne kasar Sin ta tsaya tsayin daka wajen gina ingantaccen tsarin ilmi a matakin farko na tsarin ilmin kasar. Domin gina tsarin ilmi mai inganci, dole ne a bada fifiko wajen bibiyar hanyoyin yin garambawul a sahun gaba, don a samu nasarar gudanar da yin sauye sauyen a ragowar fannonin ilimin, in ji shugaba Xi. Ya kuma bukaci a kara himma wajen horar da mutane masu basira wadanda za su bayar da muhimmiyar gudunmawa wajen bunkasa ci gaban kasa da samar da wani babban yanayi na dogaro da kai. (Ahmad Fagam)