logo

HAUSA

Illa za ta koma kan masu yin adawa da Sin

2021-03-19 20:35:47 CRI

Illa za ta koma kan masu yin adawa da Sin_fororder_1

Yayin taron watsa labaran da aka shirya a jiya Alhamis a jihar Xinjiang, Gulbostan Rozi, wadda ta zo daga yankin Kashgar na jihar, ta bayyana cikin fushi cewa, “Kamar yadda karin maganar ‘yan kabilar Uygur ya bayyana, idan ka jefa dutse sama, kila ne dutse zai fado a kanka, wato dai mayaudari Adrian Zenz ka kula da kanka, kada dutse ya fado a kanka.”

To, ko wane ne Adrian Zenz? Wasu rukunonin masu adawa da kasar Sin suna kiran wannan ‘dan asalin kasar Jamus mai shekaru 47 da haihuwa da “kwararren mai nazarin harkokin Xinjiang”, amma hakika shi mai baza jita-jita ne kawai kan jihar.

A cikin ‘yan shekarun da suka gabata, ya kan wallafa wasu rahotanni na adawa da kasar Sin a fadin duniya, inda har ya samu goyon bayan rukunonin masu adawa da kasar Sin, kuma kasancewarsa mamban asusun tunawa da wadanda suka shan wahalhalun kwaminis, wanda Amurkawa masu sassaucin ra’ayi suka kafa, ana iya cewa, yana yin aiki ne na adawa da kasar Sin.

Illa za ta koma kan masu yin adawa da Sin_fororder_2

Alkaluman da aka fitar sun nuna cewa, tun daga shekarar 2018, gaba daya Adrian Zenz ya rubuta rahotanni sama da goma, wadanda ke shafawa jihar Xinjiang ta kasar Sin bakin fenti. Ga wasu jimlolin da ya rubuta, “aikin tilastawa” da “tiyatar hana haihuwa da aka tilastawa mata” da “kare al’adu” da “kisan kare dangi”, dukkansu suna tsorata masu karantawa, amma abu mai ban mamaki shi ne, wannan masanin batun Xinjiang bai taba zuwa jihar ba ko sau daya.

Yanzu haka mazauna jihar Xinjiang na fadin gaskiyar ainihin yanayin da suke ciki, inda jami’ai, da wakilan bangaren addini, da fararen hula na jihar, suka karyata rahotanin karya da Adrian Zenz ya rubuta, yayin taron watsa labarai da aka shirya.

Migit Timit, mai noman auduga a jihar Xinjiang, ya bayyana cewa, “Muna noman auduga a gonakinmu, kuma mun samu kudin shiga daga aikin, shin ina dalilin da ya sa za a kira aikinmu aikin tilastawa?”

Rahotannin sun nuna cewa, wasu kamfanoni da mazauna na jihar Xinjiang, sun riga sun kai Adrian Zenz kara a kotu, domin kiyaye kima da moriyarsu. Ko shakka babu, za a hukunta Adrian Zenz bisa doka, da rukunonin dake adawa da kasar Sin, wadanda ke goyon bayansa. (Jamila)