logo

HAUSA

Sin da Amurka na matukar bukatar juna domin dorewar ci gaban su

2021-03-18 16:44:53 CRI

Sin da Amurka na matukar bukatar juna domin dorewar ci gaban su_fororder_0318-3

A ‘yan kwanakin nan, hankula sun karkata ga batun ganawar da manyan jami’an kasashen Sin da na Amurka za su yi a birnin Anchorage na jihar Alaskan kasar Amurka.

Masharhanta dai na ganin wannan tattaunawa, wata dama ce ga sassan biyu, ta zantawa gaba da gaba, da nufin kamo bakin zaren manyan matsalolin dake kara raba kawunansu.

Tuni dai mahukuntan kasar Sin suka sha nanata fatansu, na ganin sassan biyu sun kafafa dangantakar su yadda ya kamata, ta yadda al’ummun su za su amfana, kuma duniya baki daya, ta ci gajiya daga dorewar bunkasar manyan kasashen biyu.

Yayin da duniya ke kara amincewa da muhimmancin rungumar cudanyar dukkanin sassa, ta yadda za a gudu tare a tsira tare, salon wasu kasashen duniya na sake bullo da cacar baka, da sukar manufofin cikin gidan wasu kasashe, na zamewa wannan buri da ake da shi “kadangaren bakin tulu”. Sin ta sha nanata bukatar kauracewa sabani, da kin jinin wani yanki ko wata kasa, da nuna adawa da ci gaban wani bangare, ko tsoma baki cikin harkokin gidan wata kasa, wanda hakan ko shakka babu “shiga sharo ba shanu ne”.

Alal hakika dai, ba wanda zai musanta irin yadda Sin ke fatan ganin an dinke dukkanin baraka tsakaninta da bangaren Amurka, musamman idan aka yi la’akari da tarin manufofinta na inganta cudanya da dukkanin sassan kasa da kasa, burin da a karshe shi ne, samar da duniya mai kyakkyawar makomar bai daya ga dukkanin bil Adama.

Sai dai fa wannan buri zai yi wahalar cika, idan har Amurka da kawayen ta, suka ci gaba da aiwatar da manufofin rarraba kawunan kasa da kasa, da nunawa wasu bangarori yatsa.

Idan an yi duba na tsakani, game da salon diflomasiyyar sabuwar gwamnatin Amurka ta yanzu, ana iya cewa, shugaba Joe Biden bai rungumi daukacin manufofi masu tsauri da tsohon shugaban kasar Donald Trump ya fara aiwatarwa ba, ta fuskar alakar Amurka da sauran sassa, sai dai kuma duk da haka, dagewar da ya yi cewa, Sin wata kasa ce dake yiwa Amurka barazana ta fuskar takara, na nuna cewa “Akwai sauran rina a kaba”, game da fatan da ake da shi na sassauta yanayin dangantakar kasashen biyu.

A wannan gaba da ake tunkarar shawarwari tsakanin manyan jami’an kasashen biyu, idan har sassan za su dakatar da sabani game da cinikayya da batun takara, da kakabawa juna takunkumi, hakan zai ba su damar mayar da hankali ga muhimmin kalubale dake addabar su, da duniya baki daya, kamar sauyin yanayi, da farfado da tattalin arzikin duniya, bayan shawo kan cutar COVID-19. (Saminu Alhassan)