logo

HAUSA

Sanarwar Ministocin Harkokin Wajen Kasashen G7 Ba Za Ta Yi Tasiri Ko Kadan Ba

2021-03-13 21:50:07 CRI

Sanarwar Ministocin Harkokin Wajen Kasashen G7 Ba Za Ta Yi Tasiri Ko Kadan Ba_fororder_微信图片_20210313215032

Bayan hukumar kolin kasar Sin dake tsara dokoki ta zartas da kudurin tsarin zabe na yankin musamman na Hong Kong, a ranar 12 ga wata, ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar G7 sun bayar da wata sanarwa, inda suka kara bata sunan kasar Sin, bisa zarginsu na cewa wai matakin da Beijing ta dauka ya soke ikon Hong Kong na tafiyar da harkokinsa da kansa da damar da kowa yake da ita ta shiga zabe, sun kuma bukaci kasar Sin da ta dauki matakai bisa hadaddiyar sanarwa dake tsakaninta da Burtaniya.

Abin da ya kamata a lura shi ne, tun bayan gabatar da manufar "kasa daya, mai tsarin mulki biyu", babbar manufarta ita ce kiyaye dinkewar kasa daya da mutunta cikakken yankin kasa, da kuma tabbatar da wadata da zaman karko a yankin Hong Kong. Wato, "kasa daya" sharadi ne da kuma tushen "tsaruka biyu". Gwamnatin kwamitin tsakiya ta kasar Sin tana gudanar da cikakken mulki a kan Hong Kong bisa kundin tsarin mulki da babbar dokar yankin, kuma Hong Kong yana da ikon tafiyar da harkokinsa a karkashin ikon da kwamitin tsakiya ya damka masa.

An lura cewa, kyautata tsarin zabe na Hong Kong da majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ta yi, bai canja aya ta 45 da ta 68 dake cikin babbar dokar yankin ba ko kadan, wadanda suka shafi tabbatar da kowa na iya shiga zabe. Wannan ya nuna cewa, ba za a canja muradun Hong Kong na tabbatar da kowa na iya shiga zabe bisa hakikanin halin da yankin ke ciki ba.

Game da hadaddiyar sanarwar dake tsakanin Sin da Burtaniya da suka ambata kuwa, ba ta da tushe ko kadan. Sanarwar ba ta dorawa Burtaniya alhaki kan harkokin Hong Kong da ikon tsoma baki cikin harkokin yankin ba, bayan maido da shi karkashin ikon kasar Sin.

An gano cewa, kudurin kyautata tsarin zaben da majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ta zartas ya samu goyon baya sosai daga wajen mazauna yankin Hong Kong da ma kasashen duniya. (Mai fassara: Bilkisu)