An tono wani wuri dake cikin makabartar Saqqara
2021-03-09 13:55:59 CRI
A kudancin Alkahira na kasar Masar, an tono wani wuri dake cikin makabartar Saqqara. Makabartar da aka gano a wannan karon ta hada da haikalin jana’izar matar Sarki Taiti, Sarauniya Nart, da kuma sanduna, akwatin gawa da gawawwaki daga lokacin Sabuwar Masarautar, wadanda tarihinsu ya wuce shekaru 2500. (Bilkisu)