logo

HAUSA

Duniya na sa ran tarukan CPPCC da NPC da Sin ta kaddamar za su samar da zarafi mai kyau

2021-03-04 20:03:52 CRI

Duniya na sa ran tarukan CPPCC da NPC da Sin ta kaddamar za su samar da zarafi mai kyau_fororder_微信图片_20210304200327

Taron CPPCC da NPC da Sin ta kan gudanar a kowace shekara, ya zama wata taga ga duniya ta duba kasar Sin.

Wata kafar yada labarai ta Latin Amurka ta ba da labarin cewa, kasancewar wannan shekara ita ce ta cika shekaru 100 da kafuwar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kuma shekara ta farko ta aiwatar da shirin shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin na 14, manufofi da kudurorin da za a tsara a gun tarukan za su zama masu muhimmanci matuka.

Kafofin yada labarai na duniya sun ce, Sin ta samu bunkasuwa fiye da yadda aka yi tsamani a shekarar bara. Duniya kuma na sa ran kasar Sin za ta ba da gudunmawarta wajen ingiza bunkasuwar duniya, duk da ganin mawuyancin hali da duniya ke ciki yanzu, musamman ma matakan da Sin za ta dauka a tarukan, a fannin kara bude kofarta ga waje, da yin kirkire-kirkire, da raya tattalin arzikin kiyaye muhalli, wadanda za su samarwa duniya damammaki masu kyau na samun bunkasuwa tare.

Aikin mafi muhimmanci a cikin taro na bana shi ne, bincike da kuma tattaunawa kan shirin shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin na 14, da kuma daftarin burin da ake fatan cimmawa nan da shekarar 2035. A sa’i daya kuma, rahoton ayyukan gwamnati zai ba da amsa ga yadda Sin za ta tsara muradunta na samun bunkasuwar tattalin arziki da al’umma a bana, da yadda za a aiwatar da su. Kafar yada labarai ta Reuters ta ba da labarin cewa, wannan rahoto, da kuma shirin ya fi jawo hankalin duniya.

Bude kofa ga kasashen waje, ya fi jawo hankalin kafofin yada labarai a bana. Yin kirkire-kirkire wani bangare ne na daban, dake ingiza bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin. Kafar yada labarai ta Birtaniya Lexology, ta ba da labarin cewa, Sin tana da shirin sauya hanyar da take bi daga daddaden tsarin samar da kayayyaki, zuwa ta amfani da kimiya da fasaha ta hanyar yin kirkire-kirkire. Sabon shirin raya tattalin arzikin da Sin ta dauka, wato dogaro da sabbin sana’o’i da masana’antu da kasuwanci, suna kawo babban amfani mai yakini ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya.

Alkaluman da hukumomi masu ruwa da tsaki suka bayar na nuna cewa, yawan jarin dake shafar tattalin arzikin kiyaye muhalli zai kai triliyan 12, wanda ya kai kashi 8% na dukkan GDPn kasar kafin shekarar 2025. An yi kiyasin cewa, wannan adadi zai kai kashi 10% a shekarar 2035. Bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin mai kiyaye muhalli ba za ta amfana kasar Sin kawai ba, har ma za ta kawo amfani mai yakini ga duniya baki daya.

An ce a shekarar 2021, Sin ta bude sabon shafi na raya kasa mai bin tsarin mulki na gurguzu mai sigar musamman. Za a shaida yadda kasar Sin za ta girka, da kuma aiwatar da ajandun raya kasar a wannan shekara da muke ciki, da kuma cikin shekaru 5, har ma shekaru 15 masu zuwa.

Ana kuma sa ran za ta samarwa duniya damammaki masu kyau. Ko shakka babu, kasar Sin tana da shirye-shirye da tsare-tsare masu kyau, za ta kuma zama wani karfi mai inganci, na tabbatar da bunkasuwar duniya. (Amina Xu)