logo

HAUSA

Karya Fure take ba ta ’ya’ya

2021-03-03 19:53:40 CRI

Karya Fure take ba ta ’ya’ya_fororder_微信图片_20210303155949

Da alamu har yanzu Amurka da wasu ’yan kanzaginta na kasashen yamma ba su san cewa, annabi ya faku ba, inda suke ci gaba da yada bayanan karya ko neman shafawa kasar Sin bakin fenti ta hanyar kirkirar labaran bogi, wai ana aikata kisan kare dangi a yankin Xinjiang na kasar Sin. Abin tambaya shi ne, yaushe masu kitsa irin wadannan bayanai suka je jihar? Idan mai fadar magana wawa ne, to majiyinta ba wawa ba ne.

Wannan nema ya sa wani shafin watsa labarai mai zaman kansa na Amurka mai suna “Grayzone” ya wallafa wani rahoto, don karyata irin wadannan karairayi da gutsiri tsoma da Amurka ke yadawa mai taken “Zargin da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta yada game da kisan kare dangi a kasar Sin”. Babban editan shafin Max Blumenthal, ya ce, ya karyata rahoton ne, saboda bayanan cin zarafi da zargi marasa tushe da masu tsattsauran ra’ayin rikau suka tattara, don bata sunan kasar Sin. Inda ya karyata rahoton da Zheng Guoen wani mai ra’ayin rikau na addini ya tsara.

A ranar 24 ga watan da ya gabata, wakiliyar babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin (CGTN) Lin Xin, ta zanta da Max Blumenthal, inda ya shaida mata cewa, rahoton Zheng Guoen, karya ce kawai ya kitsa, don ya haifar da masifar da bai san inda za ta tsaya ba. Amma kowa ya debo da zafi, to, bakinsa.

A takaice dai Edita Max ya ce, ya karyata sharhin da Zheng ya rubuta ne a wannan karo, don ya sanar da duniya cewa, Amurka tana son yin amfani da bayanan yaki ne, domin samun goyon bayan jama’a kan samar da agajin jin kai a Syria ko Libya, amma tuni duniya ta gano makirci da sakamakon tallafin jin kan da take ikirari, wanda hakan tamkar keta hakkin dan-Adam ne matuka. A don haka, tana son ta fakewa da wannan batu ta shiga yankin Xinjiang don ta aikata irin ta’asar da ta yi a wadancan wurare. To Kifi yana ganinka mai Jar koma.

Shin idan ana kisan kare dangi a Xinjiang ko hana haihuwa ko tilastawa mutane aikin dole kamar yadda makaryaci Zheng ya rubuta, ta yaya za a samu karuwar haihuwa ko kudaden shiga na mazauna yankin, har ma rayuwarsu ta inganta?

A karshe, Edita Max ya bukaci Amurka, da ta daina neman bata sunan kasar Sin a dukkan fannoni, ko neman bullo da wani salon lalata dangatakar diflomasiya tsakanin kasashen biyu ko wani sabon yakin cacar baka. Abin da duniya take bukata a halin yanzu, shi ne cudanyar bangarori daban-daban. Amma wanda bai ji gari ba, to, zai ji hoho. (Ibrahim Yaya)