logo

HAUSA

Ya kamata a magance tushen matsalolin dake sa bakin haure barin kasashensu na asali

2021-03-02 17:24:58 CRI

Ya kamata a magance tushen matsalolin dake sa bakin haure barin kasashensu na asali_fororder_微信图片_20210302164803

Ya kamata a magance tushen matsalolin dake sa bakin haure barin kasashensu na asali_fororder_微信图片_20210302164806

Batun bakin haure ko ’yan ci rani dake hankoron zuwa Turai daga nahiyar Afrika ta hanyar ratsa kasar Libya, dadadden batu ne da ya ki ci ya ki cinyewa, wanda kuma ke ciwa duniya tuwo a kwarya.

Ko a ranar Lahadin da ta gabata, jami’an tsaron tekun Libya, sun ceto  bakin haure kimanin 181 daga gabar tekun yammacin kasar. A cewar rundunar sojin ruwan kasar, mutanen sun fito ne daga kasashen Afrika daban-daban, kuma cikinsu akwai mata 15 da yara 10.

A cewar hukumar kula da kaura ta duniya IOM, a shekarar 2020 kadai, bakin haure 323 sun mutu, wasu 417 kuma sun bata, yayin da aka ceto 11,891 daga nutsewa cikin tekun Bahr Rum.

Jami’in hukumar Federico Soda, ya taba bayyana cewa, ana samun wadannan mace-mace masu tayar da hankali ne, sakamakon tsananin tashin hankali da matsanancin talauci dake tilastawa mutanen yunkurin tsallake tekun Bahr Rum zuwa kasashen Turai, da kuma gazawa wajen daukar matakan dakile yawaitar kwararar ’yan ci ranin.

Hakika, wannan batu ne mai matukar tayar da hankali ganin yadda wadannnan mutane ke galabaita da shiga mawuyacin hali, har ma da asarar rayuka.

Ba a shafe lokaci mai tsawo sai an samu batun bata ko mutuwar ’yan ci rani a tekun na Meditereniya. Duk da sanin hadarin dake tattare da tafiyar, mutane ba sa dainawa, a ganinsu, abun da suke hankoron samu, ya fi hadarin da suke fuskanta girma.

Girke jami’an tsaro ko cafke wadannan mutane ba zai taba zama mafita ga yunkurinsu ba, dole ne a lalubo bakin zaren, wato a samo ainihin dalilin da ya sanya zama a kasashensu na asali ke gagararsu.

Bincike ya nuna cewa, yawancin bakin haure na barin kasashensu ne saboda batutuwa kamar na talauci da rashin ingancin tsarin kiwon lafiya da ilimi da abinci da ruwa mai tsafta, har ma da matsalolin da suka shafi sauyin yanayi da muhalli, ga kuma rikicie-rikice da tashe-tashen hankula da suke ci gaba da gudana.

Yayin da bakin haure da dama suka samu ingantuwar rayuwa ta wannan hanya, akwai adadi mai yawa daga cikinsu, wadanda ke fadawa cikin mawuyacin hali, inda su kan gamu da matsalolin take hakkokinsu na bil Adama tare da fuskantar barazanar kame a kasashen da suke bi ko suka nufa da fyade da sauransu. Idan ma suka yi nasarar isa inda suke da burin zuwa, rayuwa cikin kwanciyar hankali kan yi musu wahala kasancewar ba su bi ka’ida ba, inda samun kulawar lafiya ko ingantacciyar rayuwa ke gagararsu.

Wajibi ne gwamnatocin da kulawa da rayuwar al’umarsu ta rataya a wuyansu, su lalubo hanyoyin magance tushen matsalar ta yadda al’ummominsu za su ji dadin kasancewa a kasashensu na asali da bada tasu gudunmawa wajen raya kasa, da kuma uwa uba kare rayuka da mutuncinsu.  (Fa’iza Mustapha)