logo

HAUSA

Sake shiga yarjejeniyar Paris da Amurka ta yi na bukatar ta kara daukar matakai masu amfani

2021-02-20 21:55:39 CRI

Sake shiga yarjejeniyar Paris da Amurka ta yi na bukatar ta kara daukar matakai masu amfani_fororder_微信图片_20210220215315

Jiya Jumma’a, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya fitar da wata sanarwa, inda a cikinsa aka ce, a jiyan Amurka ta sake shiga yarjejeniyar Paris wadda take tinkarar matsalar sauyin yanayi a duniya.

A matsayinta na babbar kasar dake fitar da iska mai gurbata muhalli a duniya, a karshen shekara ta 2020, Amurka ta sanar da janyewarta daga yarjejeniyar Paris, bisa hujjar dake cewa wai yarjejeniyar ta kara matsa mata lamba a fannin tattalin arziki. Janyewar Amurka ba kawai ta kawo babbar illa ga kokarin aiwatar da yarjejeniyar Paris ba, har ma ita kanta ta dandana kudarta. A irin wannan halin da take ciki, sake dawowar ta yarjejeniyar abu ne da ya cancanci yabo. Amma daukar hakikanan matakai domin aiwatar da ita ya fi bullo da wata sanarwa muhimmanci.

Sake shiga yarjejeniyar Paris da Amurka ta yi na bukatar ta kara daukar matakai masu amfani_fororder_微信图片_20210220215321

Har wa yau, kasashe masu hannu da shuni, ciki har da Amurka, bai dace ba su dauki batun sauyin yanayi a matsayin wata hujjar dake kawo tsaiko ga ci gaban kasashe masu tasowa. Maimakon haka, su bi ka’idojin dake cikin yarjejeniyar sauyin yanayi ta Majalisar Dinkin Duniya, da kara rage fitar da iskar dake gurbata muhalli, da samar da goyon-baya a fannin kudade da fasahohi da kwarewa ga kasashen dake fama da matsalar sauyin yanayi, ta yadda za’a kafa wani sabon tsarin tinkarar matsalar.

Muna fatan Amurka za ta fahimci muhimmiyar ma’anar yarjejeniyar Paris ga samar da dauwamammen ci gaban ‘yan Adam, da daukar sahihan matakai don bada gudummawa ga tinkarar matsalar sauyin yanayi, da kuma daukar nauyin dake wuyanta, musamman a matsayinta na kasa mafi karfin tattalin arziki a duniya.(Murtala Zhang)