logo

HAUSA

An kaddamar da cibiyar kirkire-kirkire da hadin gwiwa ta Sin da Afrika a Wuhan

2021-02-19 10:34:31 CRI

An kaddamar da cibiyar kirkire-kirkire da hadin gwiwa ta Sin da Afrika a Wuhan, babban birnin lardin Hubei na tsakiyar kasar Sin a jiya Alhamis.

Cibiyar za ta samar da dandamali biyu ta kafar intanet da wanda ba na intanet ba, domin inganta kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha da hadin gwiwa, da zuba jari ta fuskar samar da kayayyaki da musayar fasaha tsakanin matasan bangarorin biyu.

Za kuma a kafa wasu kananan cibiyoyin binciken kimiyya da musayar fasaha, sannan za a shirya ayyukan hadin gwiwa a bangarorin kimiyya da fasaha da za su amfanawa bangarorin biyu.

Cibiyar muhimmin bangare ne na bunkasa kwarewa karkashin hadin gwiwar Sin da Afrika. Za ta kuma gudanar da shirye-shiryen domin saukaka hada ingantattun fasahohi da musayar ra’ayi a bangarori daban-daban tsakanin al’ummun Sin da Afrika. (Fa’iza Mustapha)