logo

HAUSA

Yadda Fasahohin Zamani Suka Kara Inganta Bikin Bazara

2021-02-17 19:19:14 CRI

Yadda Fasahohin Zamani Suka Kara Inganta Bikin Bazara_fororder_0217-1

Yadda Fasahohin Zamani Suka Kara Inganta Bikin Bazara_fororder_0217-2

Al’ummar Sinawa na ci gaba da shagulgulan bikin bazara, inda galibin Sinawa suka zabi gudanar da bikin tare da iyalansu, ta hanyar amfani da kafofin yanar gizo, tare da yin sayayya ko ziyartar gidajen adana kayan tarihi ta kafofin yanargizo, a wani mataki na hana yaduwar annobar COVID-19.

Tun kafin bikin na bana, mahukunta suka bukaci jama’a da su gudanar da bukukuwan a wuraren da suke ayyuka, maimakon komawa garuruwan su kamar yadda aka saba yi a baya. Duk da rashin komawar jama’a garuruwansu don saduwa da iyalansu, masu fashin baki na cewa, fasahohin zamani, kamar 5G mai ba da damar amfani da yanar gizo cikin sauri, ta taimakawa Sinawan wajen gudanar da wannan muhimmin biki cikin farin ciki da annashuwa, duk da cewa, ba haka aka so ba, wai kanin miji ya fi miji kyau.

Alkaluma sun nuna cewa, daga ranar 11 zuwa 16 ga watan Fabrairun wannan shekara, a manhajar Tiktok dake nuna gajerun bidiyo, an kalli sakwannin gaisuwar sabuwar shekarar gargajiya ta Sinawa sama da sau biliyan 70.3. Kazalika a watan Janairun da ya gabata, yawan mutane da suka yiwa ‘yan uwansu, ko abokai sayayya ta manhajar Hema ya kai sama da kaso 30%. Har ila yau, a jajiberin ranar bikin bazarar, manhajar Meituan ta samu karuwar odar masu sayayya ta yanar gizo da sama da kaso 85 bisa dari, idan an kwatanta da bara.

Tun bayan da mahukuntan Sin suka bayar da lasisin fara kafa tashoshin intanet na 5G a watanYunin shekarar 2019, ya zuwa karshen shekarar bara, an kafa sama da tashoshin 5G 700,000, da kuma kananan tashoshin hada fasahar sama da miliyan 200.

Kaza lika an tsara kafa karin tashoshin 5G sama da 600,000 a wannan shekara ta 2021. Wanda hakan ke nuna cewa, gaba daya, Sin za ta fadada ginawa, da samar da hidimomin fasahar 5G masu gamsar da bukatun al’ummar ta.

Wannan ya nuna cewa, duk da cewa, Sinawa basu koma garuruwansu ba kamar yadda aka saba bisa al’ada a lokacin bikin bazara, a hannu guda, fasahohin zamani sun kara taka muhimmiyar rawa, wajen kara armashin bikin bazara na bana, ta hanyar biyan bukatun al’ummar Sinawa cikin sauki a fannoni daban-daban, kamar sayayya, yawon shakatawa, sada zumunta da makamantansu. Wai a rashin uwa akan yi uwar daki.(Ibrahim Yaya)