logo

HAUSA

Bikin bazarar bana ya kasance sabon mafarin samun wadata ga Sinawa

2021-02-16 19:57:52 CRI

Bikin bazarar bana ya kasance sabon mafarin samun wadata ga Sinawa_fororder_1

A gabannin bikin bazara wato bikin sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, wata manomiya a kauyen Atulier na gundumar Zhaojue ta yankin Liangshan na lardin Sichuan na kasar Sin ta bayyana cewa, dole ne a shirya babbar liyafa wadda kunshi nama da kaji da awara domin murnar bikin, saboda bikin bazara na bana zai kasance bikin bazara na farko bayan da ita da ‘yan uwanta dake kauyenta suka fita daga talauci.

A shekarar 2020, manoman kauyen Atulier sun kaura daga kauyensu dake kan tuddai zuwa sabbin gidajen kwanan da gwamnatin ta gina musu a kasa, inda ake samar musu da ruwan fanfo da iskar gas, lamarin da ya alamta cewa, an cimma burin kawar da talauci daga duk fannoni a fadin kasar Sin. Kamar yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana, burin gwamnatin kasar Sin mai sigar gurguzu, shi ne samar da jin dadin rayuwa ga al’ummarta, ba tare da barin kowa a baya ba.

Bikin bazarar bana ya kasance sabon mafarin samun wadata ga Sinawa_fororder_2

A karshen shekarar bara, bisa mataki na karshe, kasar Sin ta yi nasarar kawar da talauci a kauyuka 1113 dake cikin gundumomi 52 masu fama da talauci, daga nan kasar Sin ta cimma burinta na kawar da talauci a fadin kasar daga duk fannoni bayan kokarin da take yi a cikin shekaru 8 da suka gabata, lamarin da ya taka rawar gani ga babban sha’anin yaki da talauci a duk duniya.

Yanzu haka gwamnatin kasar Sin tana samarwa mutanen da suka fitar da kansu daga kangin talauci karin damammakin samun ci gaba, domin tabbatar da sakamakon da suka samu. Bisa shawarwarin da aka gabatar a cikin shirin raya kasa na shekaru biyar biyar na 14, kasar Sin za ta kara mai da hankali kan aikin samun wadata a cikin shekaru biyar masu zuwa, kuma ana sa ran burin nan na samar da wadata ga daukacin al’ummun kasar ta Sin zai samu babban ci gaba nan da shekarar 2035.(Jamila)