logo

HAUSA

Labaran Bogi Ba Za Su Samun Amince A Nan Kasar Sin

2021-02-12 17:49:00 CRI

 

Labaran Bogi Ba Za Su Samun Amince A Nan Kasar Sin_fororder_EB17B22D-7C4D-4038-A451-D91B9E4E8103

Yau Juma’a, gwamnatin kasar Sin ta yanke shawarar kin amincewa, da rokon sashin labaran duniya na gidan rediyon na BBC ta fuskar watsa shirye-shiryensa a kasar Sin, domin kafar ta sabawa ka’idar ayyukan watsa labarai. BBC ta mai da martani da cewa, tana matukar rashin jin dadi kan hakan. Wata mai magana da yawun kafar ta nuna cewa, BBC kafa ce mafi samun amincewa a duniya wajen watsa shirye-shiryen radiyo, tana kuma yada labaran kasa da kasa bisa gaskiya da adalci ba tare da nuna bambancin ra’ayi ba ko kadan ba? Har ma wani jami’I mai kula da harkokin diplomasiyya na Birtaniya Dominic Raab ya ce, matakin da Sin take dauka na kawo cikas ga ‘yancin kafofin yada labarai.

Shin ko BBC ba ta jin kunya?

BBC ta harhada wani bidiyo mai taken “Komawa birnin Wuhan”, amma a cikin wannan bidiyo an rage haske, da saka wasu kida mai sanya fargaba, da hada wasu bidiyoyi da ta dauka, wadanda da ba su da alaka da juna, don bayyana ra’ayinsu, cewa wai wannan wuri ne aka fara samun asalin cutar COVID-19. Ban da wannan kuma, ta kan watsa wasu labarai marasa tushe, kan batun jihar Xinjiang, tana nuna cewa wai ba a karewa jama’ar Xinjiang hakkin Bil adama.

A hakika dai, masanan kiwo lafiya na kasa da kasa sun kai ziyarar birnin Wuhan, Sin ta bude wurare da dama don su sa ido da yin bincike, duk wannan ya nuna cewa, Sin tana fatan taka rawarta a fannin neman asalin wannan cuta, don magance ta tun da wuri. Kaza lika Sin ba ta boye komai kan wannan batu.

Ban da wannan kuma, kafofin yada labarai da dama sun taba ziyartar jihar Xinjiang, inda suka ganewa idanunsu yadda jama’ar Xinjiang ke zaman rayuwa. Mazauna da dama kuma suna bayyana hakikanin zaman rayuwarsu mai cike da farin ciki a wurin a gaban mutane.

Amma BBC ba ta yi la’akari da gaskiya ko hakikanin hali da ake ciki ba, ta kirkiro labarai yadda take so, don bautawa wasu ‘yan siyasar Birtaniya.

Idan ba a manta ba, kwanan baya, Birtaniya ta sanar da soke izinin gidan talibijin na kasa da kasa na kasar Sin a Birtaniya. A wannan karo kuma, Sin ta mayar da martaninta.

Duk matakan da BBC ke dauka na baza jita jita, nufi ne na shafawa kasar Sin bakin fenti, amma ba za a amince da labaran bogi ba, kuma ba zai dakatar da bunkasuwar kasar Sin ba ko kadan. (Amina Xu)