logo

HAUSA

Xi Jinping ya gabatar da muhimmin jawabi a taron koli na kasar Sin da kasashen tsakiya da gabashin Turai

2021-02-10 11:43:03 CRI

Xi Jinping ya gabatar da muhimmin jawabi a taron koli na kasar Sin da kasashen tsakiya da gabashin Turai_fororder_hoto

Jiya Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya shugabanci taron koli na kasar Sin da kasashen tsakiya da gabashin Turai ta kafar bidiyo a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Shugabanni da manyan jami’ai, da wasu wakilai na kasashen tsakiya da gabashin Turai da suka hada da kasar Bosnia, da kasar Czech, da kasar Poland, da kasar Albania, da kasar Romania da dai sauransu sun halarci wannan taro.

A yayin taro, shugaba Xi Jinping ya gabatar da muhimmin jawabi mai taken “Mu hada kanmu, mu kuma nemi ci gaba bisa ayyukan da muka yi a baya, domin bude wani sabon shafin hadin gwiwa a tsakaninmu”.

Dangane da wannan jawabi, abokiyar aiki Maryam Yang na dauke da Karin bayani…

Cikin jawabinsa, Xi Jinping ya jaddada cewa, kasar Sin da kasashen tsakiya da gabashin Turai suna yin hadin gwiwa bisa ka’idojin yin shawarwari tare, da adalci, da nuna fahimtar juna, da kuma yin kirkire-kirkire, lamarin da ya kasance abin koyi ta fuskar habaka hadin gwiwa a tsakanin sassa daban daban. Kasar Sin tana fatan ci gaba da habaka hadin gwiwa tsakaninta da kasashen tsakiya da gabashin Turai bisa halin da muke ciki, domin cimma moriyar juna, da karfafa dunkulewar dukkanin bil Adama kamar yadda ake fata.

A yayin wannan taro, an kuma gabatar da “Shirin hadin gwiwar kasar Sin da kasashen tsakiya da gabashin Turai na birnin Beijing na shekarar 2021” da “Bayanin sakamakon da aka cimma a taron kolin kasar Sin da kasashen tsakiya da gabashin Turai”.

Xi Jinping ya ce, an shafe shekaru 9 ana hadin gwiwa a tsakanin kasar Sin da kasashe tsakiya da gabashin Turai, cikin wadannan shekaru 9, Sin da kasashen tsakiya da gabashin Turai sun cimma nasarar daidaita kalubaloli iri daban daban cikin hadin gwiwa, yayin da ake tabbatar da wasu ka’ijojin hadin gwiwa a tsakaninsu, wadanda suka samu amincewa da karbuwa daga kasashen da abin ya shafa.

Ka’ida ta farko ita ce, yin shawarwari tare kan yadda za a aiwatar da harkoki. Ta biyu kuma ita ce, samar da sakamako masu gamsarwa ga bangarori masu hadin gwiwa. Ta uku ita ce, nuna fahimtar juna, da bude kofa domin neman ci gaba tare. Ta karshe kuma ita ce, neman bunkasuwa ta fuskar yin kirkire-kirkire.

Xi Jinping ya ce,“Mu habaka tunaninmu, da yin gwaje-gwaje, domin hada shirin hadin gwiwa a tsakanin sassa daban daban da shirin “Ziri daya da hanya daya” tare, da kuma shimfida yarjejeniyar hadin gwiwa da aka kulla, bisa shawarar “Ziri daya da hanya daya” a dukkan yankunan da abin ya shafa.”

A ganinsa, muna cikin wani lokaci mai cike da kalubaloli iri-iri, don haka ya kamata kasa da kasa su hada kansu wajen daidaita wadannan kalubaloli.

Yana mai cewa,“A bara, dangantakar dake tsakanin Sin da Turai ta bunkasa kamar yadda ake fata, a gabannin matsalar yaduwar annobar cutar COVID-19. Bangarorin biyu sun kammala shawarwari game da yarjejeniyar zuba jari tsakanin Sin da Turai bisa lokacin da aka tsara, da karfafa dangantakar abokantaka tsakanin Sin da Turai, wajen yin hadin gwiwa ba tare da bata muhalli ba, da kuma yin hadin gwiwar harkokin sadarwa. Kana, bangarorin biyu sun dukufa wajen kare tsarin hadin gwiwa a tsakanin sassa daban daban, da kuma fuskantar kalubaloli cikin hadin gwiwa. Hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen tsakiya da gabashin Turai, wani muhimmin bangare ne a fannin raya dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Turai, kuma bunkasuwar dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu, zai haifar da sabbin damammaki ga hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen tsakiya da gabashin Turai.”

Bugu da kari, Xi Jinping ya kuma gabatar da shawarwari guda hudu, game da yadda za a ci gaba da raya hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen tsakiya da gabashin Turai.

Da farko, ya ce, mu fuskanci kalubalen cutar numfashi ta COVID-19 tare, da karfafa aniyarmu ta cimma nasarar yaki da cutar cikin hadin gwiwa. Ya dace a karfafa mu’amalar dake tsakaninmu a fannonin yin kandagarki da yin rigakafin cutar, da kuma tattaunawa kan habaka hadin gwiwar likitancin gargajiya, da kyautata yanayin kiwon lafiya, domin gina wani shirin kiwon lafiya ga dukkanin bil Adama.

Na biyu, ya ce, mu mai da hankali kan yin harkokin tafiye-tafiye a tsakanin bangarorin biyu, da musayar hajoji. Yana fatan za a gaggauta ayyukan gina layin dogo a tsakanin kasar Hungary da Serbia da dai sauran shirye-shiryen da abin ya shafa, yayin da raya tafiye-tafiyen jiragen kasa a tsakanin Sin da Turai yadda ya kamata.

Na uku, ya ce, mu karfafa ayyukan tallafawa juna, Kasar Sin na shirin shigowa da kayayyaki da darajarsu ta zarce dala biliyan 170, daga kasashen na tsakiya da gabashin Turai a cikin shekaru biyar masu zuwa, da nufin habaka shigowa da kayayyaki daga kasashen.

Na karshe ya ce, ana mai da hankali kan neman ci gaba ba tare da bata muhalli ba, domin gina wata makoma mai kyau. Ya kamata a inganta hadin gwiwar kasa da kasa wajen tinkarar sauyin yanayi, da zurfafa hadin gwiwa a fannonin raya tattalin arziki ba tare da bata muhalli ba, da makamashi masu tsabta. (Maryam Yang)